'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗalibin BUK, Sule, Da Ya Kammala Digiri Da 1st Class

'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗalibin BUK, Sule, Da Ya Kammala Digiri Da 1st Class

  • 'Yan bindiga sun halaka, Sule Mathew, wani dalibi da ya kammala digirinsa a Jami'ar Bayero ta Kano da First Class
  • Miyagun sun halaka Sule tare da wasu fasinjoji a Ekwulobia, a hanyarsa ta zuwa Anambra don ganin iyayensa
  • Abokan karatun marigayin da yar uwarsa sun tabbatar da rasuwarsa inda suka ce yana hanyar zuwa Anambra ne tare da maigidansa

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Sule Mathew, dalibin da ya kammala digirinsa da First Class a bangaren nazarin sadarwa kuma mai koyon makamashin aiki da PRNigeria a hanyarsa na zuwa Jihar Anambra tare da wasu fasinjoji.

Mr Mathew, wanda ya karanci Information and Media Studies, ya kammala digirinsa ne da first class daga Faculty of Communication, Jami'ar Bayero ta Kano, yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗalibin BUK Da Ya Kammala Digiri Da 1st Class
'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗalibin BUK Da Ya Kammala Digiri Da First Class. Hoto: PRNigeria
Asali: Twitter

An kashe shi tare da wasu fasinjoji a Ekwulobia, daya daga cikin manyan biranen Jihar Anambra bayan Akwa, Onitsha da Nnewi, rahoton PRNigeria.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kai gawarsa babban asibitin Ekwulobia kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Abokin karatun Mathew ya tabbatar da mutuwarsa

Wani abokin karatun Mathew kuma mai koyon makamashin aiki a PRNigeria, Salis Manager, ya ce Mr Mathew yana shirin zuwa sansanin horas da masu yi wa kasa hidima NYSC.

Mr Salis ya ce:

"Mathew na cikin dalibai na farko da suka fara koyon makamashin aiki a PRNigeria a Kano a 2019. Mahaifinsa ya rasu a watan Yuni, watanni kafin jarrabawarsa na karshe, kuma ya kammala da sakamako mafi daraja a tsangayar mu a Augustan 2021 kuma yana shirin zuwa NYSC mako mai zuwa."
"Yana hallartan wani shirin bada horaswa na kawo sauye-sauye da karfafa demokradiyya ga matasa - Gidan Yanci. Yana hanyarsa zuwa Anambra daga Abuja ne yan bindige suka tare motarsu," a cewar Gambo Ibrahim, wani abokin Mathew na kusa da suke zaune tun lokacin da suke Diploma.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Yar uwarsa ta tabbatar da rasuwarsa

Jemila Mathew, yar uwarsa ta tabbatar da cewa Mathew yana tafiya ne tare da mai gidansa da wasu fasinjoji ciki har da direban motan.

"Bayan tare su, yan bindigan sun bude musu wuta, suka kashe dukkansu illa direban da ya tsira. Mun gaza samunsa a waya, mun aika hoton Sule zuwa dakin ajiyar gawa sai aka tabbatar mana yana cikin wadanda aka kashe," In ji ta.

Mr Mathew dan asalin Jihar Kogi ne. Yana daya daga cikin wadanda suka kafa hostutors.com, wani shafin intanet da ke sadar da masu son koyon darrusa da malamai.

PRNigeria ta rahoto cewa har lokacin wallafa wannan rahoton gawarsa na asibiti a Ekwulobia.

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Kara karanta wannan

Yawancin matasan da suka kammala karatun digiri ba sa iya ayyukan da aka basu, Pantami

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164