Amaechi: Osinbajo ya amince da kudin kayan jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri a FEC

Amaechi: Osinbajo ya amince da kudin kayan jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri a FEC

  • Majalisar zartarwa ta FEC ta yi wani zama a ranar Laraba 16 ga watan Fubrairu 2022 a Aso Villa
  • A zaman da Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, an amincewa ma’aikatar Rotimi Amaechi kashe $2m
  • Za a batar da wadannan kudi ne domin sayen karafun da za ayi amfani da su a titunan jirgin kasa

Abuja - Majalisar zartarwa ta kasa ta amince a kashe fam $2.8m domin sayen wasu kayan aikin da za a bukata a dogon Ibadan-Kano da na Farakwal-Maiduguri.

Ministan sufuri na tarayya, Rotimi C. Amaechi ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da manema labarai bayan taron FEC da aka yi na wannan makon.

Jaridar Premium Times ta ce Rotimi C. Amaechi ya shaidawa ‘yan jarida cewa za a bukaci wadannan kaya wajen aiki da kuma kula da titin jiragen kasan.

Kara karanta wannan

N-Power: Gwamnatin Tarayya za ta gwangwaje matasa 300, 000 da kudin jari inji Minista

“Na samu yarjewar Ministoci na sayen kayan aiki da na kula da sababbin dogo da za ayi na Ibadan-Kano da na Fatakwal-Maiduguri a kan $2, 810, 574, 064.92.”
“Don haka za mu canza duk karafan gare-garenmu. Da su ake amfani wajen aiki da jiragen kasa da taragonsu.” - Rotimi Amaechi
Jirgin kasa
Jirgin kasa a Ibadan Hoto: freedomradionig.com
Asali: UGC

Rahoton ya ce wannan kudi da aka bada ya hada da kason haraji da gwamnati za ta cire na 7.5%.

Jawabin Ministan ya zo ne bayan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman makon nan saboda shugaba Muhammadu Buhari ya yi tafiya.

Harin da aka kai a filin jirgi

Jaridar NNN ta ce Ministan ya yi magana a game harin da aka ce an kai wa wasu fasinjojin jirgin kasa a garin Kogi. Amaechi ya ce ba a tashar jirgi abin ya faru ba.

Kara karanta wannan

Kusoshin Gwamnati za su amsa tambayoyi a Majalisa kan zargin cuwa-cuwar albashi

“Abin da na samu shi ne ba a filin jirgi ba ne, abin ya faru ne a hanyarsu ta fita daga tashar. Ba a taba kai mana hari a filin jirgi ba, amma bai nufin ba za ayi bincike ba.”

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya godewa ‘yan jarida da suka bijiro masa da wannan magana saboda ayi bincike, ya ce akwai bukatar ya zama akwai ‘yan sanda su na gadin filin jirgi.

Yajin-aiki a makarantu

An ji yadda kungiyar COEASU ta ja-kunnen Gwamnati, ta ce ko a cika alkawuran da aka yi mata a shekarar 2009, ko a ga barkewar yajin-aiki a makarantun FCE.

Kungiyar ta ce ana nuna mata tsantsar rashin girmamawa saboda irin dattakun su wajen sasantawa da gwamnati, hakan ya sa ake yi mata kallon rauni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng