Za'a ci tarar duk wanda aka kama da gajeren wando cikin Harami da Masallacin Madina N55,000

Za'a ci tarar duk wanda aka kama da gajeren wando cikin Harami da Masallacin Madina N55,000

Hukumomin a kasar Saudiyya sun sanar da sabon tarar da za'a ci mutumin da aka sake kamawa sanye da gajeren wando cikin Masallatai mafi daraja biyu a Musulunci.

Legit ta samun labarin hakan a Shafin Masallatan Makkah da Madina, Haramain Sharifain.

Sanarwar tace za'a yi waje da duk wanda aka kama kuma a cisa tarar Riyal 500, wanda yake N55,000 a kudin Najeriya.

Masallacin Madina
Za'a ci tarar duk wanda aka kama da gajeren wando cikin Harami da Masallacin Madina N55,000 Hoto: Haramain Sharifain

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng