Da duminsa: Shugaba Buhari ya amsa goron gayyata zuwa jamhuriyar Czech

Da duminsa: Shugaba Buhari ya amsa goron gayyata zuwa jamhuriyar Czech

  • A cikin shekarar nan ta 2022, Shugaba Buhari zai tafi ziyara jamhuriyyar Czech dake Turai
  • Wannan ya biyo bayan gayyatar da Shugaban kasar Czech yayi masa na musamman kuma ya amsa
  • Buhari da Milos Zeman sun hadu ne a taron gamayyar kasashen Turai dake gudana yanzu haka a kasar Beljika

Brusesels - Shugaba Muhammadu Buhari ya amsa goron gayyatar da shugaban kasar jamhuriyyar Czech, Milos Zeman, na ziyartar kasar Turan a wannan shekara ta 2022.

Wannan ya faru ne a zaman diflomasiyyar da ya gudana tsakanin Buhari da Milos Zeman ranar Alhamis a Brussels, kasar Beljika.

A zaman, shugabannin kasashen biyu sun amince a karfafa zumunta tsakaninsu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Jamhurriyar Czech
Da duminsa: Shugaba Buhari ya amsa goron gayyatar zuwa jamhurriyar Czech Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

IBB ga 'yan siyasa: Kar ku yi wasa da hadin kan 'yan Najeriya

Shugaban kasar Jamhurriyar Czech ya bayyana amincewarsa da Najeriya a matsayin jarumar kasa a nahiyar Afrika kuma ya bayyana niyyar hada kai da ita wajen harkar makamai, da karkafa tsaro.

Bayan haka ya gayyaci Ministan Lafiyan Najeriya wani taron kasashe da zai gudana a Mayu 2022 kuma ya gayyaci Shugaba buhari kasar ya kawo ziyara.

Shugaban Buhari ya amince da gayyatar kuma ya amsa, hakazalika ya umurci ministan Lafiya, Dr OSagie Ehanire, ya halarci taron a Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng