An kama wani Mutumi da zargin tafka wa diyarsa mari har ta mutu a jihar Jigawa

An kama wani Mutumi da zargin tafka wa diyarsa mari har ta mutu a jihar Jigawa

  • Yan sanda sun kama wani magidanci ɗan kimanin shekara 40 bisa zargin bugun ɗiyarsa Salima Hannafi, har lahira a jihar Jigawa
  • Bayanai sun nuna cewa magidancin, Hannafi Yakubu, ya tafka wa yarinyar mari ne, kuma Allah ya karbi rayuwarta a karamar hukumar Babura
  • A halin yanzu, Kakakin yan sanda na jihar yace hukumar yan sanda na cigaba da aikin bincike kan lamarin

Jigawa - Rundunar yan sanda reshen jihar Jigawa, ta kama wani magidanci ɗan shekara 40 bisa zargin kashe ɗiyarsa a ƙaramar hukumar Babura, jihar Jigawa.

Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya fitar ranar Alhamis a Dutse, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Shiisu ya ce lamarin ya faru ranar 12 ga watan Fabrairu, 2022 a ƙauyen Achiya, bayan mutumin ya shararawa yarinyar yar shekara 11 mari.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan abubuwa 5 da suka faru da jarumin dan sanda Abba Kyari tun farkon tuhumarsa

Taswirar jahar Jigawa
An kama wani Mutumi da zargin tafka wa diyarsa mari har ta mutu a jihar Jigawa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa sanadin wannan marin da ya mata, yarinyar mai suna Salima Hannafi, ta rasa rayuwarta a wurin da ya mare ta.

Kakakin yan sandan ya ce:

"A ranar 12 ga watan Fabrairu, 2022 da misalin ƙarfe 10:30 na safe, wani ya kawo mana rahoton cewa, a wannan rana wani mai suna Hannafi Yakubu ɗan shekara 40 ya kashe diyarsa."
"Majiyar ta bamu bayanin cewa Hannafi ya yi amfani da hannunsa ya daki ɗiyarsa, Salima Hannafi, yar shekara 11 a ƙauyen Achiya, ƙaramar hukumar Babura."
"Sanadin haka yarinyar ta mutu nan take. Sun kai mamaciyar babban Asibitin Babura domin duba ta, a can likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa. Mun ɗauki hotunan gawar sannan muka bayar aka mata jana'iza."

Wane matakin yan sanda ke ɗauka kan lamarin?

Kara karanta wannan

Kano: An kama mutum 5 kan zargin kashe wata matar aure a gidanta

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa a halin yanzun hukumar yan sanda na cigaba da bincike kan lamarin kafin ɗaukar mataki.

A wani labarin na daban kuma Matar Aure ta maka mijinta a Kotu saboda ya ƙi amincewa sun yi aure

Wata mata ta gurfanar da wani mutumi a gaban kotu kan yaƙi amincewa an ɗaura musu aure da jimawa a jihar Kaduna.

Mijin yace ya na da alaƙa da matar amma ta bariki, amma ba su kai ga auren juna ba kamar yadda ta yi ikirari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262