Ko PDP ta so, ko ta ki, sai APC ta lashe zaben 2023: Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa

Ko PDP ta so, ko ta ki, sai APC ta lashe zaben 2023: Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ovie Omo-Agege ya bayyana cewa ko ta kaka sai jam'iyyar APC ta yi waje da PDP a zaben 2023
  • Agege na cikin masu neman takarar gwamnan jam'iyyar Delta a zaben 2023 karkashin jam'iyyar APC
  • A gefe guda, Sanata Nwaboshi wanda bai dade da komawa APC ba yace babu lungun magudi da bai sani ba

Delta - Mataimakin Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ovie Omo-Agege, a ranar Laraba ya bayyana cewa ko jam'iyyar adawa ta PDP ta so, ko ta ki, sai APC ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Omo-Agege ya bayyana hakan ne a bikin rantsar da sabbin shugabannin jam'iyyar APC, reshen jihar Delta, rahoton Vanguard.

Sanatan wanda ke wakiltan mazabar Delta ta tsakiya kuma yake niyyar takarar gwamnan ya bayyana cewa lokaci ya yi da za'a kwace jihar daga hannun PDP.

Kara karanta wannan

Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa - Kungiyar Ibo

Yace:

"Mu share sabanin dake tsakaninmu, ku yiwa yan takararku magana saboda manufarmu itace doke Okowa da duk wanda yake niyyar kakaba mana."
"Al'ummar Delta zasu zabi wanda suke so matsayin gwamna da wakilai a 2023. Ba mutum daya zai zaba ba."

Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa
Ko PDP ta so, ko ta ki, sai APC ta lashe zaben 2023: Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa Hoto: NGRSenate
Asali: Twitter

Sanata Nwaboshi wanda yayi magana a taron yace babu lungun magudin zabe a jihar Delta da bai sani ba.

A cewarsa, PDP na yiwa akuyoyi rijistan zabe gabanin 2023.

Yace:

"Na san suna (PDP) tunani da shiri amma ina tabbatar muku da cewa babu abinda zasu shirya da ban sani ba, babu lungun magudin da ban sani ba."
"Ina rokon mambobin APC su hada kai don waje da PDP a 2023."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng