Ba zan yi tsokaci kan matsayar ASUU a kan farfesanci na ba, Pantami
- Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Ali Isah Pantami ya ce ba zai yi tsokaci kan tuhumar farfesancinsa da ASUU ke yi ba
- Kamar yadda ministan Buharin ya bayyana, aiki ya kai shi gidan gwamnati kuma manema labarai su tambaye shi kan ma'aikatarsa ba batun ASUU da FUTO ba
- A cewarsa, shi dan kasa ne mai kiyaye dokoki, kamar yadda aka sani FUTO ta garzaya kotu, don haka ba shi da hurumin cewa komai
FCT, Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Ali Pantami, a ranar Laraba ya ki yin tsokaci kan matsayar kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'i a kan karin matsayin da jami'ar fasaha ta tarayya da ke Owerri ta yi masa zuwa farfesa.
A ranar Litinin da ta gabata, kungiyar malaman masu koyarwa na jami'o'i ta kwatanta karin matsayin da jami'ar ta yi wa ministan da karantsaye ga doka, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin da manema labaran gidan gwamnati suka bukaci ministan ya yi tsokaci kan lamarin, Pantami ya cigaba da cewa: "Babu tsokaci".
Ya ce:
"A kan tambayar ku ta biyu, ba ni da tsokaci, babu tsokaci kuma babu tsokaci. Wannan ita ce matsayata. Aiki ya kawo ni wurin nan, ku tambaye ni kan aikin. Duk abinda ya shafi ma'aikatar sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, zan iya amsa muku domin abinda ya kawo ni nan kenan."
"Makarantar da kuka fadi suna kotu. A matsayina na jami'in gwamnati, kun san me kotu ke nufi a wurina? Ya dace ku sani kuwa. Saboda ni dan kasa ne mai bin dokoki, ba zan yi tsokaci ba, ina fatan kun fahimta, babu tsokaci."
Kisan Hausawa dillalan shanu a Kudu: Kungiyoyin Arewa sun fusata, sun tura gargadi ga gwamnatin Abia
Isa Pantami ko albashi bai karba hannun jami'ar FUTO, ASUU ta shiga taitayinta - MURIC
A wani labari na daban, kungiyar kare hakkin Musulmai MURIC ta caccaki kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU bisa watsi da nadin Ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami, matsayin Farfesa.
MURIC ta bayyana bacin ranta ne ta bakin Diraktanta, Farfesa Ishaq Akintola, ranar Talata, 15 ga Febrairu, 2022.
Zaku tuna cewa ASUU ta yi watsi da matsayin Farfesa da aka bai wa ministan harkokin sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dakta Isa Pantami.
Kungiyar, bayan taron majalisar zartasawa ta da ya gudana ranar Litinin, ta bayyana baiwa Pantami Farfesa a matsayin, "karan tsaye ga doka."
Asali: Legit.ng