Mambobin IPOB da ESN ne ke kulla-kullar bata mun suna, Abba Kyari ya magantu

Mambobin IPOB da ESN ne ke kulla-kullar bata mun suna, Abba Kyari ya magantu

  • Abba Kyari ya yi zargin cewa haramtacciyar ƙungiyar awaren IPOB da tawagar mayaƙanta ESN ne ke kulla kullan ganin bayansa
  • A cewar mataimakin kwamishinan yan sandan da aka dakatar, sun sha alwashin bata masa suna saboda ya addabe su a kudu
  • Kwamitin binciken da IGP ya kafa ya miƙa rahoto kuma tuni aka miƙa ga hukumar jin daɗin yan sanda ta ƙasa

Abuja - Mataimakin kwamishinan yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ya yi ikirarin cewa haramtacciyar kungiyar IPOB da ESN suke da hannu wajen jefa shi cikin wannan halin.

Daily Trust ta rahoto cewa Kyari yace sun fito da dukkan ƙarfin su domin ganin bayansa saboda ya matsa musu lamba a yankin kudu maso gabas.

Abba Kyari ya yi wannan zargin ne ya yin da kwamitin bincike bisa jagorancin mataimakin Sufetan yan sanda (DIG), Joseph Egbunike, ya titsiye shi da tambayoyi a hedkwatar yan sanda dake Abuja.

Kara karanta wannan

Gurbattacen Fetur: Ba mu san haka zai faru ba, a yi mana afuwa, Shugaban NNPC ya bada hakuri

DCP Abba Kyari
Mambobin IPOB da ESN ne ke kulla-kullar bata mun suna, Abba Kyari ya magantu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Furucinsa na cikin rahoton da kwamitin ya miƙa wa Sufeta Janar na yan sandan ƙasa, Usman Alƙali Baba, wanda daga baya aka miƙa wa hukumar jin daɗin yan sanda (PSC).

Yace haramtacciyar kungiyar IPOB da kuma mayaƙanta ESN sun fito da dukan ƙarfin su domin ganin sun kai shi ƙasa, saboda ya addabe su a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Kyari, wanda bai musanta saba wasu dokokin hukumar yan sanda ba, ya fuskanci fushin kwamitin kasancewar an masa gargaɗi kan aikata haka a baya.

A cikin rahoton, Kyari ya ce:

"Duk kokarin IPOB/ESN ne na ganin bayana da sunan da na yi, sun sha alwashin rusa ni baki ɗaya saboda na addabe su a yankin kudu maso gabas."

Shin kwamitin ya amince da ikirarin Kyari?

Kara karanta wannan

Hotunan takalmi mafi tsada a duniya ya bayyana a birnin Dubai, kudinsa N8bn

Sai dai kwamitin binciken ya yi watsi da kalaman Abba Kyari, inda ya nuna cewa duk borin kunya ne da kokarin kare kansa.

Kazalika kwamitin ya shawarci a rage masa matsayi daga babban mataimakin kwamishina (DCP) zuwa karamin mataimakin kwamishina (ACP).

Duk wani kokarin jin ta bakin hukumar jin daɗin yan sanda ta ƙasa game da rahoton binciken Kyari ya ci tura.

Duk kira ta wayar salula da aka yi wa kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, bai ɗaga ba, kuma bai turo amsar sakon karta kwana da aka aika masa ba.

A wani labarin kuma Daga karshe, Tsohon gwamna ya bayyana jam'iyyar da ya koma bayan ficewa daga PDP

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, yace ya shiga jam'iyyar SDP kuma zai nemi takarar gwamna a zaɓen 18 ga watan Yuni.

Oni ya sanar da cewa jiga-jigan manyan jam'iyyun APC da PDP na goyon bayan takararsa ta gwamnan Ekiti.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262