Kusoshin Gwamnati za su amsa tambayoyi a Majalisa kan zargin cuwa-cuwar albashi

Kusoshin Gwamnati za su amsa tambayoyi a Majalisa kan zargin cuwa-cuwar albashi

  • ‘Yan Majalisa sun kira taro a game da zargin da ake yi na taba albashin mutane a manhajar IPPIS
  • A karshen zaman, majalisa ta bukaci Ministar kudi, shugaban ICPC, da wasu su bayyana a gabanta
  • Shugaban majalisa, Femi Gbajabiamila ya ce za a kama duk jami'in da ya yi masu kunnen-kashi

Abuja - A ranar Talata, 15 ga watan Fubrairu 2022, majalisar wakilan tarayya ta bukaci jami’an gwamnati su zo gabanta domin su yi mata wasu karin-haske.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa an gayyaci Ministar kudi, tsare-tsare da kasafin tattalin arziki, Dr Zainab Ahmed ta kare zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya.

Sauran wadanda aka gayyata sun hada da babban akawun gwamnatin Najeriya, da mai binciken kudin gwamnati da kuma shugaban hukumar bincike ta ICPC.

Haka zalika shugaban hukumar FCC da jami’in da ke kula da IPPIS za su bayyana a majalisar.

Kara karanta wannan

Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

Majalisa ta kira zama

An cin ma wannan matsaya wajen wani taro da aka yi a majalisa inda aka ji ta bakin al’umma a game da zargin barnar da ake tafkawa a karkashin tsarin IPPIS.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An shirya wannan zaman ne da nufin magance satar da ake zargin jami’an gwamnati su na yi ta manhajar IPPIS da aka kirkiro domin saukaka biyan albashi.

'Yan majalisa
'Yan majalisar wakilan tarayya Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

Doguwa ya wakilci Femi Gbajabiamila

Da yake jawabi a zaman, shugaban majalisar wakilai na kasa, Rt. Hon Femi Gbajabiamila ya koka a kan yadda shugabanni hukumomi suka yi watsi da gayyatarsu.

Shugaban masu rinjaye a majalisa, Hon. Alhassan Ado-Doguwa ne ya wakilci Gbajabiamila a zaman. Doguwa ya ce akwai bukatar a hada-kai domin gyara a kasa.

A madadin shugaban majalisar, Doguwa ya ce za su cigaba da kokari wajen ganin an yi amfani da fasaha domin magance matsalolin da ake samu a aikin gwamnati.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko

Kwamiti ya yi barazana

‘Yan majalisar sun bayyana cewa jami’an da aka gayyata kadai za su iya yi wa kwamitin bayani sosai a kan kudin da ake zargin an wawura daga asusun gwamnati.

Shugaban kwamitin hadakar da aka kafa a majalisa, Hon. Nicholas Garba ya yi barazanar cewa za su bada umarni a cafke duk jami’in da ya ki hallara a gaban na su.

Binciken NPA

A jiya an ji cewa a karshen binciken da kwamitin mutum 11 ya gudanar, an gano Hadiza Bala Usman ba ta karkatar da N165bn daga asusun hukumar ta NPA ba.

Duk da babu abin da yake nuna Bala Usman ta saci kudi, kwamitin ya tabbatar da cewa zargin ta da ake yi da rashin da’a gaskiya ne, ta na bijirewa Ministan sufuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng