Wahalar man fetur: N600 ake sayar da litan mai yanzu a Abuja

Wahalar man fetur: N600 ake sayar da litan mai yanzu a Abuja

  • Mutane na cigaba da kokawa kan karanci da tsadar man fetur a jihohin Najeriya yayinda abin ke kara tsananta
  • Wannan tsadar mai ya haifar da hauhawar farashin sufuri da kayan masarufi a kasuwanni
  • Mutan birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa yanzu litan man fetur ya kai N600 hannun yan bumburutu

Bayan fama da hauhawar farashin kayan masarufi da yan Najeriya ke yi, an shiga fama da wahala da tsadar man fetur sakamakon matsalar gurbataccen mai da aka kawo Najeriya.

Maimakon abin yayi sauki, yan Najeriya na kokawa kan yadda abubuwa ke kara tsanani kulli yaumin.

Daily Trust ta ruwaito cewa yanzu a birnin tarayya Abuja yan kasuwar bayan fagge wanda akafi sani da yan bumburutu na sayar da litan man fetur N600.

A Kano, Legas da Fatakwal, farashin ya na tsakanin N250 zuwa N400 ga lita yayinda masu motocin haya suka tafka karin kudin mota.

Kara karanta wannan

Man Fetur Zai Wadata Zuwa Karshen Wata, Za Mu Raba Lita Biliyan 2, Shugaban NNPC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wahalar man fetur: N600 ake sayar da litan mai yanzu a Abuja
Wahalar man fetur: N600 ake sayar da litan mai yanzu a Abuja

Layukan mai sun ki raguwa

Duk da umurnin da kamfanin NNPC ta baiwa gidajen manta su rika sayar da mai har cikin dare, an waye gari layukan motoci masu bukatar mai karuwa yake.

Wasu sun yi zargin cewa gidajen man na boyewa ne don sayarwa yan bunburutu a farashi mai tsada.

Man Fetur Zai Wadata Zuwa Karshen Wata, Za Mu Raba Lita Biliyan 2, Shugaban NNPC

Babban manajan darektan hukumar NNPC, Mele Kyari ya ce rarraba man fetur zai tabbata cikin makwanni kadan masu zuwa, Vanguard ta ruwaito.

Manajan ya ce zuwa karshen wannan watan za a rarraba Lita miliyan 2.1 na man fetur don ya yalwatu a kasar nan

Kyari ya bayar da wannan tabbacin ne yayin wani taro da kwamitin rikon kwarya ta majalisar wakilai wacce take bincike dangane da gurbataccen man fetur din da aka shigo da shi kasar nan kamar yadda Vanguard ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng