Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

  • Kotun Majistire a Kaduna ta bada umarnin a Bulale wani matashin ɗan kasuwa da ya saci buhunan gishiri da kuma na Fulawa
  • Wanda ake zargi da aikata lamarin, Nasiru Ahmed, bai wahalar da kotu ba, ya amsa laifinsa tare da rokon Kotu ta masa sassauci
  • Yan sanda sun gurfanar da shi gaban Kotu ne bayan samun korafin abin da ya faru daga hannun mai shagon da akai wa sata

Kaduna - Wata Kotun Majistire a Kaduna ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 25, Nasiru Ahmed, hukuncin bulala bakwai kan satar buhunan Gishiri guda biyar.

Matashin mi sana'ar Tireda ta saye da siyarwa na zaune ne a Anguwar Tudun Wada, dake cikin birnin Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

An gurfanar da Ahmad ne a gaban Kotu, bisa tuhumar fasa shago da kuma aikata sata a shagon.

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun Shari'a Ta Tura Kishiyoyi 2 Zuwa Gidan Yari Saboda Faɗa Kan Mijinsu, Mijin Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Sake Su Duka

Bulala
Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna Hoto: freedomonline.com.ng
Asali: UGC

Alƙalin Kotun, Mai Shari'a Ibrahim Emmanuel, ya yanke wa matashin ɗan kasuwan hukunci, bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kuma ya roki kotu ta sassauta masa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda shari'ar satar gishirin ta kasance

Tun da farko dai, mai gabatar da ƙara daga hukumar yan sanda, Mista Chido Leo, ya shaida wa alƙalin Kotun cewa wani mutumi mai suna, Malam Abdulmalik Lateef, ne ya kai korafin lamarin Caji Ofis dake Kawo.

Ya bayyana cewa a ranar 7 ga watan Fabrairu, mutumin ya kawo ƙarar shiga masa shago da kuma satar wasu kayayyakinsa.

Mista Leo ya tabbatar da cewa wanda ake ƙara ya fasa shagon Malam Lateef a kasuwar Kawo, kuma ya yi awon gaba da buhunan gishiri 4 da kuma na Fulawa biyu.

Yace:

"A ranar 7 ga watan Fabrairu, Malam Abdulmalik Lateef ya kawo mana kara cewa Nasiru Ahmed, ya shiga shagonsa a kasuwar Kawo, ya sace masa buhunan Gishiri 5 da kuma buhunan Fulawa biyu."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya watsa wa gwamnonin APC biyu ƙasa a ido, ya ƙi amincewa da bukatarsu

Shugaba Buhari ya watsa wa wasu gwamnonin APC biyu ƙasa a Ido, ya umarci su bi matakai matukar suna son ya amince.

Rahoto ya nuna cewa gwamnonin sun garzaya ga Buhari ne domin ya goyi bayan ɗan takarar da suke so ya zama shugaban APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262