ASUU: Ba dole sai an shafe wata ba, a kwana 7 za mu dawo aiki idan Gwamnati ta ga dama
- Malaman jami’a sun ce ba dole bane yajin-aikin da suka fara sai ya dauki kwanaki 30 da aka bada
- Wani jagora na kungiyar ASUU ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta iya takaita yajin-aikin
- Christopher Piwuna ya ce NIREC za ta iya amfani da wannan lokaci domin a samu a cinma maslaha
Abuja- Kungiyar Academic Staff Union of Universities ta malaman jami’a ta ce yajin-aikin makonni hudun da ta tafi zai iya zuwa karshe a mako guda.
Wani mataimakin shugaban kungiyar ASUU na kasa, Dr. Christopher Piwuna ya bayyana wannan a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV.
Duk da zuwa yanzu kwana daya kurum aka ci, Christopher Piwuna ya ce malaman jami’a na iya janye yajin-aiki idan gwamnatin tarayya ta yi abin da ya dace.
“Mu na sa ran wannan yajin-aikin jan-kunnen na wata daya zai ba majalisar addinai ta NIREC damar cika alkawarinta na yin magana da wanda suka dace.”
“Idan suka yi abin da ya kamata, to ba za mu yi wata guda mu na wannan yajin-aikin ba. Za mu iya dawowa aiki a cikin mako guda.” - Dr. Christopher Piwuna.
NIREC ta sha alwashi za ta zauna da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da sauran masu rike da mukamai, ta tursasa su a kan a biyewa ASUU bukatunta.
Malamin jami’ar ya yi wannan bayani ne a shirin nan na Sunrise Daily a safiyar ranar Talata, 15 ga watan Fubrairu 2022. Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoton.
Shekara daya da rabi babu labari
Piwuna yake cewa shekara daya da rabi kenan da gwamnati ta ce su kawo tsarin da za a bi wajen raba N170bn da za a fitar domin bunkasa jami’o’i, har yau shiru.
Mataimakin shugaban na ASUU ya ce sun kawo shawara a 2021 cewa duk bayan watanni uku, gwamnatin tarayya ta saki N42.5bn, amma ba a biya ko sisi ba.
Har ila yau, malamin na jami'ar Jos ya ce gwamnatin tarayya ta ki biyan malaman jami’a bashin alawus din da suke binta tun shekarar bara, ga shi an shiga 2022.
Ganin zai yi wahala a iya fito da N1.3tr ne a yanzu, ASUU ta ce a biya kudin gutsun-gutsun. Piwuna ya ce shi ma duk da haka, wannan ya gagari gwamnati.
Yajin aiki: Can da su gada - Kungiya
Dazu aka ji wata kungiya mai suna Progressive Academic Staff Union of Universities, tana cewa babu abin da zai sa a rufe jami’ar Chukuwuemeka Odumegwu Ojukwu.
Shugaban wannan kungiyar, Farfesa Osita Chiaghanam ya ce ba za su biyewa wata kungiya ko daidaikun mutane wajen shiga yajin-aikin da ba zai amfani kowa ba.
Asali: Legit.ng