‘Yan Majalisa sun cire ayyuka masu amfani, sun jefa kwangilolin N887bn a kasafin 2022

‘Yan Majalisa sun cire ayyuka masu amfani, sun jefa kwangilolin N887bn a kasafin 2022

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisa tayi garambawul a kan dokar kasafin kudin 2022
  • A wata wasika da Shugaban kasa ya aikawa ‘Yan majalisa, ya ce sun cusa ayyuka a kasafin kudi
  • Buhari ya bukaci a goge duk wasu kwangilolin da ‘Yan majalisa suka kakaba ba tare da bin doka ba

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya soki majalisar tarayya a kan cire wasu muhimman ayyuka da suka yi daga cikin kundin kasafin kudin bana.

Jaridar This Day ta rahoto Mai girma Muhammadu Buhari yana zargin cewa ‘yan majalisa sun yi cushen ayyukan N887bn a kasafin shekarar nan ta 2022.

Har ila yau, shugaban kasar ya na kuma zargin ‘yan majalisar kasar da shiga shara babu shanu a aikin bangaren masu zartarwa, wanda ba su da hurumi.

Kara karanta wannan

Buhari ya mika wa majalisa karin kasafin kudi, ciki har da na tallafin man fetur N2.557tr

A cewar shugaba Buhari, wannan aiki da ‘yan majalisar suka yi na cusa abin da suke so a kasafin kudin, ya sabawa dokar kasa da ta ba kowa matsayinsa.

Hakan ta sa aka janye N16.59bn daga cikin kason Service Wide Vote, aka maida shi zuwa asusun majalisa.

'Yan majalisa sun yi karambani

‘Yan majalisar sun kawo wasu ayyuka a ma’aikatar sufuri da ofishin sakataren gwamnati da na shugaban ma’aikatar gwamnati, wanda dole a goge su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari
Tawagar Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Ahmad Lawan ya karanto wasikar shugaban kasar a jiya.

A wannan wasika da ya rubuta, Muhammadu Buhari ya ce akwai bukatar a soke duk wasu kwangiloli da aka samu mai-mensu a cikin kasafin 2022.

Buhari ya ce an samu kwangiloli 139 daga cikin 254 da suke cikin kundin kasafin kasar da za a bukaci a shafe su. Wadannan ayyuka za su ci N13.24bn.

Kara karanta wannan

Hadiman ‘Yan Majalisa sun sanar da Buhari badakalar da ake tafkawa a Majalisa

Takardar shugaban kasar ta kuma nemi a dawo da wasu kwangiloli hudu a ma’aikatar ruwa ta tarayya wanda aka yi lissafin aikinsu zai ci N1.4bn a 2022.

Karin N2.5tr a kasafin 2022

Hakan na zuwa ne a lokacin da Buhari ya aiko bukatarsa gaban majalisar dattawa, ya na so ayi kwaskwarima ga kasafin kudin da ya sa wa hannu a 2021.

An ji cewa a cikin wadannan kudi da za a kara, tallafin man fetur zai dauki kaso mai yawa. Gwamnatin tarayya ta na sa ran janye tallafin a Yunin bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng