Yadda kanin Abba Kyari ya karbi Naira miliyan N279 daga hannun yaran Hushpuppi

Yadda kanin Abba Kyari ya karbi Naira miliyan N279 daga hannun yaran Hushpuppi

  • Binciken da ‘Yan Sanda suka gudanar a kan Abba Kyari ya nuna akwai hannun wani ‘danuwansa
  • Ana zargin kanin Abba Kyari da karbar sama da Naira miliyan 200 daga wajen mutanensu Hushpuppi
  • Hujjojin banki sun nuna shi kan shi ‘Dan Sandan da ake bincike ya aikawa ‘danuwansa N40m a bankinsa

Abuja - Binciken ‘yan sanda ya bankado yadda Ramon Abass wanda aka fi sani da Hushpuppi da mutanensa suka aika N235, 120, 000 ga kanin Abba Kyari.

Binciken da aka yi ya kuma nuna DCP Abba Kyari wanda aka dakatar daga aiki ya tura N44m zuwa ga asusun wannan kanin na sa a lokuta dabam-dabam.

Jaridar Punch ta fitar da wani bangare na sakamakon binciken da aka yi a kan tsohon shugaban dakarun Intelligence Response Team watau DCP Abba Kyari.

Kara karanta wannan

Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

Binciken da aka gabatarwa Mai girma Ministan shari’a ya bayyana cewa akalla N279.120m suka shiga asusun bankin kanin Abba Kyari a mabambantan lokuta.

Abin da bincike ya nuna

"Sikiru Adekoya ya karbi kudi daga Hushpuppi da Efe, ya kuma aika su ga Usman Ibrahim. Adekoya ya yi kokarin karyata samun alakar kudi tsakaninsa da Hushpuppi da Efe Martins.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sai dai dole ya saduda bayan an nuna masa hujjoji daga bankinsa. “Amma bai iya bayanin kudin menene ba ko kuma abin da ya yi da su.”
Kanin Abba Kyari
'Yanuwan Abba Kyari Hoto: fij.ng
Asali: UGC
“Kamfanin Efe Martins Integrated Concept Ltd ya rika aika kudi zuwa ga Sikiru Adekoya, Usman Waziri Ibrahim, da Hussaini Ala.“

Wani daga cikin ‘yanuwan Kyari yana cikin wadanda Ala ya yi ta aikawa kudi a banki har N218, 120, 000. Sannan kuma ya samu N44m daga asusun DCP Kyari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko

Kamar yadda rahoton ya bayyana, miliyoyin kudin sun fito ne daga hannun gawurtattun ‘yan damfara irinsu Efe Martins, Usman Ibrahim, da shi Hussaini Ala.

Rahoton da aka fitar a safiyar Laraba bai iya tabbatar da cewa ko ‘danuwan jami’in tsaron da yanzu yake tsare ya rika karbar miliyoyin a madadin Kyari ba ne.

Duk da haka dai kwamitin ya samu ‘dan sandan da alaka da wadanda ake zargi da aikata laifi.

Lauya ya ba IGP shawara

Tun a jiya ku ka ji cewa wani lauya mai kare hakkin al’umma da yake aiki a garin Abuja, Pelumi Olajengbesi ya tofa albarkacin bakinsa a kan tirka-tirkar Abba Kyari.

Pelumi Olajengbesi ya ce kai Abba Kyari gaban hukumar NDLEA zai nuna za a bar gaskiya tayi aiki. Yanzu haka dai DCP Kyari ya na hannun hukuma, ana bincikensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng