Yadda muka lallasa APC a zaben Abuja, haka zamuyi mata a 2023: PDP

Yadda muka lallasa APC a zaben Abuja, haka zamuyi mata a 2023: PDP

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta lallasa APC a addadin kujerun kansila a zaben da ya gudana a birnin tarayya
  • A zaben ciyamomi kuwa, an yi kunnen jaki; PDP ta lashe uku, jam'iyyar APC ta samu lashe uku
  • Mafi takaici ga APC shine karamar hukumar Kuje inda PDP ta lashe dukkan kujerun goma

Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana farin cikin bisa nasarar da ta samu a zaben kananan hukumomin birnin tarayya Abuja da ya gudana karshen makon da ya gabata.

Kakakin jam'iyyar, Hon. Debo Ologunagba, a jawabin da ya saki ya bayyana cewa wannan nasara da PDP ta samu a Abuja na nuna yadda zasuyi nasara a 2023.

An gudanar da zabe a kananan hukumomin Abuja shida wanda ya hada da AMAC, Bwari, Abaji, Kuje, Gwagwalada, da Kwali.

Kara karanta wannan

Ku taimaka ku sake damƙa amanar Najeriya hannun APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya

Yace:

"Nasarar da Peoples Democratic Party (PDP) ta samu a kananan hukumomi uku; masu suna AMAC, Bwari da Kuje..yan nuna yadda mutane ke son mulki ya koma hannun PDP a 2023."
"Tunda aka zabi PDP ta jagoran karamar hukumar AMAC wacce ke cikin gari, yan Najeriya sun nuna cewa lallai sun yanke shawara fitittikan APC a 2023."

Jam'iyyarPDP
Yadda muka lallasa APC a zaben Abuja, haka zamuyi mata a 2023: PDP Hoto: Offical PDP
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng