'Yan Bindiga Sun Bindige Mutum Ɗaya, Sun Sace Wasu 10 a Tashar Jirgin Ƙasa a Kogi
- ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 10 tare da halaka mutum daya yayin da suka kai farmaki tashar jirgin kasa da ke Ajaokuta, Jihar Kogi
- Lamarin ya auku ne a ranar Litinin da misalin karfe 2 na rana inda ‘yan bindigan suka bayyana rike da makamai suka hau harbe-harbe ko ta ina
- Wata majiya ta shaida yadda ‘yan bindigan suka kira ‘yan uwan daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da shi suna neman Naira miliyan 20 matsayin kudin fansa
Jihar Kogi - ‘Yan bindiga sun halaka mutum daya tare da garkuwa da mutane 10 yayin da suka kai farmaki tashar jirgin kasa da ke Ajaokuta, Jihar Kogi a ranar Litinin, Vanguard ta ruwaito.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 2 na rana inda ‘yan bindigan suka bayyana rike da makamai inda suka bude wuta har harsashin bindiga ya samu wani Dennis, wanda take a wurin ya kwanta dama.
An samu bayanai akan yadda marigayi Dennis ya ke hanyar sa ta zuwa ya dauki shugaban sa na wurin aiki lokacin da ya riski ajalin sa.
Daga nan, ‘yan bindigan sun sace mutane 10 wanda yawancin su mazauna kauyen Ajaokuta ne wadanda suka je suna jiran jirgin kasa a tashar.
Har sun bukaci naira miliyan 20 wurin ‘yan uwan daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su
Wata majiya daga kauyen ta shaida yadda masu garkuwa da mutanen suka bukaci naira miliyan 20 a matsayin kudin fansar daya daga cikin wadanda suka sace.
Wani mazaunin Ajaokuta, Dele Ajala ya ce:
“Garkuwa da mutane ta sanya ‘yan uwan wasu cikin damuwa da tashin hankali. Hakan ya biyo bayan rashin tsaron kasar nan. Akwai bukatar a karo yawan ‘yan sanda a jihohi don kawo garanbawul akan matsalolin tsaro.
“Kusan kullum sai an yi garkuwa da wasu. Yanzu haka mutane sun kasa yin amanna da gwamnati saboda ta gaza samar da tsaro ingantacce.”
Jami’in hulda da jama’an ‘yan sanda ya ce bai san komai akan harin ba
Yayin da aka nemi jin ta bakin jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, William Ovye Aya, ya ce har yanzu ba a sanar da shi komai dangane da lamarin ba.
Sai dai ya yi alkawarin tuntubar wakilin Vanguard don sanar da shi da zarar ya samu cikakken bayani akai.
'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida
A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.
Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.
Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.
Asali: Legit.ng