Shugaba Buhari ya tura tawagar mutum 4 Sokoto domin taya shi ta’aziyyar jikan Sardauna
- Muhammadu Buhari ya yi magana a game da mutuwar Magajin Gari, Alhaji Hassan Marafa Danbaba
- Mutuwar Magajin Garin Sokoto ta girgiza Shugaban kasa, ya aiko tawaga ta taya shi da ta’aziyya
- Abubakar Malami ya jagoranci tawagar Ministocin da suka zo yi wa mutanen garin Sokoto ta’aziyya
Abuja - Gidan talabijin na Channels TV ta ce mai girma Muhammadu Buhari ya fito ya na alhinin mutuwar Magajin Garin Sokoto, Hassan Marafa Danbaba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa gwamnati da mutanen Sokoto ta’aziyyar mutuwar Hassan Marafa Danbaba wanda yake rike da sarautar Magajin gari.
Marigayi Hassan Marafa Danbaba jika ne a wajen Sardaunan Sokoto, Alhaji Ahmadu Bello. Firimiyan na Arewa jika ne wajen Shehu Usman Danfodio.
Rahoton ya ce shugaban kasa ya tura tawaga ta musamman da za tayi ta’aziyya a madadinsa.
Sarkin Musulmi, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Biyu Sun Hallarci Jana’izar Jikan Sardauna Da Aka Yi a Sokoto
Tawagar Abubakar Malami
Wannan tawaga ta na kunshe da Ministoci hudu a karkashin jagorancin Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnatin Najeriya, Abubakar Malami SAN.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abubakar Malami SAN ya ce Muhammadu Buhari ya girgiza da labarin mutuwar Magajin Gari, domin rashinsa ta taba jihar Sokoto ne da ma daukacin Najeriya.
Sauran ‘yan tawagar sun hada da Ministocin harkar ruwa, jiragen sama, da na ‘yan sanda Suleiman Adamu, Hadi Sirika da Muhammadu Maigari Dingyadi.
Politics Digest ta ce shugaban Najeriya Buhari ta bakin tawagar Ministocin da ya tura zuwa ta’aziyyar, ya roki Allah ya jikan wanda ya riga mu gidan gaskiya.
Jawabin Garba Shehu
Mai magana da yawun bakin Muhammadu Buhari watau Garba Shehu, ya fitar da jawabi yana cewa rashin Hassan Danbaba ya bar gibin da zai yi wahalar cikewa.
“Kullum cikin faram-faram yake da fara’a. Za a tuna da shi a matsayin jakadan al’adar masarautar Sarkin Musulmi.”
“Ina mika addu’a ta da kuma alhini ga iyalin da ya bari, gwamnati da kuma mutanen jihar Sokoto.” - Muhammadu Buhari.
Danbaba ya kwanta dama
Ku na da labari cewa a ranar Asabar dinnan da ta wuce ne Allah Ya yi wa Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Marafa Danbaba rasuwa a garin Kaduna.
Magajin Garin Sokoto, Hassan Danbaba ya cika ne bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya. Mahaifiyarsa ce babbar 'diyar Sardauna, Ahmadu Bello.
Asali: Legit.ng