Batun lalata da matan fim: Nafisa Abdullahi ta saki martani ga Sarkin waka

Batun lalata da matan fim: Nafisa Abdullahi ta saki martani ga Sarkin waka

  • Jaruma Nafisa Abdullahi ta fitar da budaddiyar wasika kan batun ana lalata da matan fim kafin a saka su shiri kamar yadda Sarkin waka yace
  • Ta bayyana cewa wannan ba karamin zargi bane kuma Naziru ya fito in har ya na da hujja da shaidu ya fallasa wadanda ke hakan ba ya zo ya na habaici ba
  • Ta yi kira ga matan masa'anatar da su fito su fadi duk wanda ya taba nemansu da latata domin babu shakka sai sun bi mata hakkin ta

Kamar yadda Legit.ng ta gano, batun da yafi yi wa 'yan Kannywood zafi a maganar sarkin waka shi ne batun lalata da mata kafin a saka su a fim inda matan Kannywood ke ta fitowa suna musanta waccan maganar da yayi.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta rubuta budaddiyar wasika cikin harshen turanci a shafinta na Instagram kuma ta kara da bayani a kasan wasikar da harshen Hausa inda ta bayyana cewa babban zargi ya fitar tunda ta na cikin matan masana'antar.

Kara karanta wannan

Na so yin shuhura da sunan karuwa a Twitter, Sabuwar Salma ta Kwana Casa'in

Batun lalata da matan fim: Nafisa Abdullahi ta saki martani ga Sarkin waka
Batun lalata da matan fim: Nafisa Abdullahi ta saki martani ga Sarkin waka. Hoto daga @nafeesat_official
Asali: Instagram

Jarumar ta yi kira ga sarkin wakan idan ya na da matsala da wani ne, ya bayyana sunansa su yi ta kare ba wai ya bata masana'antar ba baki daya.

Har ila yau, a zancenta cikin budaddiyar wasikar, ta yi kira ga matan masana'antar kan cewa duk wacce darakta ko furodusa ya taba nemanta da lalata, ta fito ta bayyana sunansa domin a magance matsalar.

Ta kara da kira ga matan da su kasance masu daraja kansu kuma duk wanda ya neme su da latata kafin ya saka su a fim, su fito su yayata shi.

A cewarta:

"A kowacce sana'a, akwai matsaloli daban-daban da mutane ke fuskanta. Akwai masu cuta, akwai kuma wadanda ake cutarwa.
"Zantuttukan da Naziru Ahmad ya yi ba karamin zargi ba ne da ba a daukarsa da sanyi ko a ina ne har da zargin zina, wanda hakan yasa na saka kaina a abinda bai shafe ni ba.

Kara karanta wannan

'Yar Najeriya ta dawo gida daga Ingila bayan shekaru 25, ta tarar mai haya ya sayar da gidanta

"Amma kuma idan aka yi la'akari da abunda ya fada, ya shafe ni tunda mace ce ni. Idan abunda ya fada gaskiya ne kuma yana da hujja da kuma shaidu, ina daga cikin mutanen da suke son su san su waye masu yin hakan.
"Tunda ya fada wa duniya ga abinda ake yi, toh karshen adalci ga wanda aka zalunta shi ne mu san su waye kuma mu dauki mataki a kansu. Don a cikin shari'armu na kasar na da ta masana'antar fim babu inda aka yadda da cewa mace ta bada kanta kafin a saka ta a fim
"Akwai dokoki da hukunci mai tsanani da za a yi wa duk wanda ya aikata hakan.
"Daga karshe kuma, duk mace da ta san an taba ce mata ta bada kanta kafin a saka ta a fim, ta yi kokarin kwatar 'yancin kanta wajen gaya mana su waye, saboda idan ba ku fito kun fada ba, ba za mu samu gyara ba. Allah yasa mu dace."

Kara karanta wannan

Dirama ta ɓarke a Kotu yayin da Amarya ta yi ikirarin Ango ya danna mata saki uku a waya

Kannywood: Batun biyan Ladin Cima dubu biyu a fim ya tada hazo a masana'antar

A wani labari na daban, mutane a shafukan sada zumunta sun dinga maganganu daban-daban kan ikirarin jaruma Ladin Cima na cewa wasu furdusoshi na biyan ta dubu biyu zuwa dubu biyar idan ta fito a fim din su.

BBC ta zanta da ita a shirin Daga Bakin Mai Ita, kuma Ladin Cima Haruna ta ce dalilinta na gaza mallakar gidan kan ta shi ne rashin samun kudi a dunkule wanda ya taba kai dubu ashirin, talatin ko hamsin a harkar fim.

Babu shakka maganganunta sun tayar da hazo inda ake ganin daraktoci da masu ruwa da tsaki na cutar 'yan wasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng