Yanzu-Yanzu: Bayan Korar Wasu Hadimanta, Buhari Ya Naɗa Wa Aisha Sabbin Hadimai Biyu
- Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wa uwargidansa Aisha Buhari sabbin hadimai biyu kamar yadda Kakakin Shugaban Kasa Garba Shehu ya sanar
- An nada Aisha Rimi a matsayin babban hadima ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin shari'a, na ofishin First Lady wato uwargidan shugaban kasa
- Sai kuma Dr Zumah da aka nada a matsayin likitan uwargidan shugaban kasa Mrs Aisha Buhari
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin karin hadimai biyu ga First Lady, Mrs Aisha Muhammadu Buhari.
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban kasar ya sallami daya daga cikin tsafin hadiman Aisha sannan aka yi wa wasu sauyin wuraren aiki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren ranar Laraba cewa Buhari ya nada Aishi Rimi a matsayin babban hadima ta musamman, sannan Dr Zabah a matsayin likitan Aisha Buhari.
Aisha Rimi
An nada Aisha Rimi a matsayin babban hadima ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin shari'a, na ofishin First Lady.
Rimi ta yi karatun digiri na aikin lauya a Jami'ar Buckingham da ke Ingila. Kuma kwararriya ce sannan tana daga cikin wadanda suka kafa African Law Practice, wadanda suka kware a kan dokokin shari'ar kasuwanci.
Dr Zabah
Hakazalika, Buhari ya amince da Dr Zabah a matsayin likitan Aisha Buhari.
Dr Zabah kwararren likita ne a bangaren 'Nuclear Medicine' kuma mamba ne na 'College of Radiologists of Nigeria and Fellow of the South African College of Nuclear Physicians'.
Shugaba Buhari ya kori hadimar Aisha Buhari, Zainab Kazeem
Tunda farko, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Muhammad Sani Zorro, dan jarida, dan siyasa kuma tsohon dan majalisa a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a bangaren harka da al'umma da tsare-tsare, a ofishin First Lady.
Shugaban kasar ya kuma amince da korar Zainab Kazeem, mataimakiya na musamman ga shugaban kasa bangaren ayyukan gida da taruruka, ofishin First Lady.
Sabon nadin da korar na cikin wata sanarwa ce ta babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a bangaren jarida da watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter.
Asali: Legit.ng