Abubuwa 6 da ya dace a sani kan Ladin Cima, jarumar da kalamanta suka tada tarzoma a Kannywood
Jarumar Kannywood, Ladin Cima ta sha caccaka a masana'antar Kannywood game da furucin da tayi kwanan nan, inda take ikirarin ba'a taba biyan ta fiye da N20,000 na wasan kwaikwayon da ta tabayi a fim daya ba.
Maganar wacce ta fusata wasu daga cikin masu mukamai a masana'antar Kannywood, ta bude faifan zantawa game da yadda ake sallama da walwalar 'yan wasan kwaikwayon a masana'antar.
Ga wasu daga cikin kalubalen da jarumar ta fuskanta wadanda kila ba kuda masaniya:
- An samu labarin yadda ta zama jarumar da ta fi dadewa a Kannywood. A wani tattaunawa, Cima ta ce, ta shigo masana'antar lokacin da babu wanda ya ke biyan ta kudin wasan kwaikwayo, kuma ta na tasowa daga Kano ta je Kaduna saboda a lokacin babu masu shirya wasan kwaikwayon a Kano.
- Cima ta yi aure tana 'yar shekara 13. Duk da bakatsiniya ce, ta yi aure a Kano, kuma ta haifi yara uku, amma abin tausayi, biyu daya daga ciki sun rasu, yarinya daya ce ta rayu.
- Jarumar ta fara wasan kwaikwayon ne bayan rasuwar mijin ta. Yayin bada labarin yadda rayuwarta ta kasance a baya, jarumar ta ce ta na kallon wasan kwaikwayo a talabijin mai nuna launin baki da fari, kuma jaruman na matukar birgeta. Amma ba ta samu damar fara wasan ba, sai bayan rasuwar mijin ta.
- Haka zalika, ta yi aiki a asibiti. Wasu daga cikin masoyan ta ba za su iya sani ba, amma jarumar ta yi aiki a asibiti a Kano na tsawon shekaru, kuma ba ta daina ba ko bayan ta fara wasan kwaikwayon. Ta yi ritaya kwanan nan.
- Ta fara wasan kwaikwayon tun kafin a san za a kafa masana'antar Kannywood saboda masana'antar bata fi shekaru 30 da kafuwa ba, ta yi wasan kwaikwayo tun kafin gidan silmar Hausa ta zama masana'antar a Najeriya.
- Bugu da kari, Cima ta kai tsawon shekaru 50 a matsayin jaruma. Fitacciyar jarumar ta ce, ta fara fim din ta na farko tun lokacin mulki soja, san da tsohon shugaban kasan Najeriya, janar Yakubu Gowon ya mulki kasar.
Kannywood: Batun biyan Ladin Cima dubu biyu a fim ya tada hazo a masana'antar
A wani labari na daban, mutane a shafukan sada zumunta sun dinga maganganu daban-daban kan ikirarin jaruma Ladin Cima na cewa wasu furdusoshi na biyan ta dubu biyu zuwa dubu biyar idan ta fito a fim din su.
BBC ta zanta da ita a shirin Daga Bakin Mai Ita, kuma Ladin Cima Haruna ta ce dalilinta na gaza mallakar gidan kan ta shi ne rashin samun kudi a dunkule wanda ya taba kai dubu ashirin, talatin ko hamsin a harkar fim.
Babu shakka maganganunta sun tayar da hazo inda ake ganin daraktoci da masu ruwa da tsaki na cutar 'yan wasa.
Asali: Legit.ng