Kisan Hanifa: Matan Arewa sun bukaci a hukunta iyaye saboda rashin kula
- Matan Arewa sun bukaci gwamnati a Najeriya ta samar da wasu dokoki da za'a rinka hukunta iyayen yara masu sakaci
- Shugabar kungiyar Matan Arewa (JMA), Hajiya Rabi Saulawa, ta ce kisan Hanifa a Kano ya zama misali, lokacin da aka sace ta tare da wa take?
- A cewarta ya kamata iyaye musamman a Arewa su rika tunawa za su yi wa Allah bayani kan yadda suka sauke nauyin yaran da ya basu
Kano - Wata ƙungiya mai suna Jam'iyyar Matan Arewa (JMA) ta yi kira da babban murya cewa a rinka ɗaukar mataki kan iyayen da suke watsi da 'ya'yan su, musamman a arewacin Najeriya.
Shugabar kungiyar JMA, Hajiya Rabi Musa Saulawa, ita ce ta yi wannan kiran yayin da take martani kan kisan Hanifa Abubakar yar kimanin shekara 5 a Kano.
Hajiya Rabi Saulawa, ta zargi wasu iyaye musamman a Arewa da rashin ɗaukar matakan baiwa 'ya'yansu kariya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shugabar JMA ta ce:
"Idan muka yi nazari kan lamarin Hanifa, na yi imanin cewa akwai rashin kula daga bangarenmu iyaye. Yarinyar da bata wuce shekara 5 ba, kuma kyakkyawa kamar Hanifa, bai kamata a barta babu mai sa ido ba."
"Ina mamakin yadda aka sace ta, mun san wanda ya yi garkuwa da ita har ya kashe ta malamin su ne, saboda haka ba zata damu ba zata amince da shi don ba baƙonta bane."
"Amma lokacin da aka ɗauke ta daga ina ta fito, wasu sunce ta dawo daga Islamiyya, shin ita kaɗai ce? Irin haka na faruwa a Arewa saboda mu iyaye mun watsar da nauyin dake kan mu."
Allah zai tambayi iyaye kan kula da yayan su - JMA
Ta ƙara da cewa a ranar Lahira, Allah zai tambayi kowane uba ko uwa dangane da nauyin da ya ɗora musu na kula da ƴaƴan su.
"Allah zai tambaye mu, yadda muka kula da yaran da muka haifa, Allah kaɗai yasan abinda ya faru da ita (Hanifa) kafin a kashe ta."
"Mahaifiyarta ta mare shi lokacin da ta ganshi, kanta ya kamata ta mara, idan nice ita kaina zan mara. Hakkina ne kula da ɗiyata amma ban yi ba, muna da sakaci kan ƴaƴan mu."
Gwamnati ta rinka hukunta iyaye masu sakaci
Daga nan kuma sai Hajiya Rabi ta yi kira ga gwamnati ta samar da dokokin da zasu rinka hukunta iyaye masu sakaci.
"Matukar ba'a kafa dokokin nan ba, to iyaye za su cigaba da nuna halin ko in kula game da nauyin kula da ƴaƴan su."
A wani labarin kuma Gwamna Tambuwal ya yi ikirarin cewa abu ɗaya ya rage wa Buhari wanda zai sa a rika tuna wa da shi bayan ya bar mulki
Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, yace abu ɗaya da ya rage shugaban ƙasa, Buhari, ya gudanar shi ne sahihi kuma karbabben zabe a 2023.
Punch ta rahoto Tambuwal na cewa ya kamata shugaba Buhari ya yi koyi da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, wajen tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe.
Asali: Legit.ng