Kannywood: Batun biyan Ladin Cima dubu biyu a fim ya tada hazo a masana'antar
- Furosodusoshi da daraktoci sun fito tare da musanta ikirarin Ladin Cima na cewa ana biyanta dubu biyu zuwa biyar ne idan ta yi fim
- Falalu Dorayi ya ce ba gaskiya ba ne don shi kan shi ya na biyanta dubu ashirin, talatin har zuwa hamsin idan ta yi masa fim
- Ali Nuhu kuwa ya ce maganganunta sun ja masa zagi, babu shakka ta yi musu kudin goro wanda ya dace ne ta banbance masu kyautata mata
Mutane a shafukan sada zumunta sun dinga maganganu daban-daban kan ikirarin jaruma Ladin Cima na cewa wasu furdusoshi na biyan ta dubu biyu zuwa dubu biyar idan ta fito a fim din su.
BBC ta zanta da ita a shirin Daga Bakin Mai Ita, kuma Ladin Cima Haruna ta ce dalilinta na gaza mallakar gidan kan ta shi ne rashin samun kudi a dunkule wanda ya taba kai dubu ashirin, talatin ko hamsin a harkar fim.
Babu shakka maganganunta sun tayar da hazo inda ake ganin daraktoci da masu ruwa da tsaki na cutar 'yan wasa.
Me daraktoci da furodusoshi suka ce?
Babu shakka wannan abu ya tada hazo inda daraktoci da furodusoshi suka fito kiri-kiri suka musanta ikirarin jarumar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Falalu A. Dorayi
Wannan ya na daya daga cikin manyan daraktoci a masana'antar kuma ya na saka Ladin Cima a fina-finansa.
Ya ce kalaman ta sun bashi mamaki matuka saboda tunda ya ke saka ta a fim, bai taba biyan ta kasa da dubu ashirin ba.
"Ba a yi kwanaki goma ba muka yi aiki na biya ta dubu talatin," a cewarsa.
Ya ce a girmanta da mutuncin da ake gani a matsayin kaka a masana'antar, babu wanda zai biya ta hakan, sai kuwa kanana masu tasowa.
Doaryi ya ce suna da fahimtar juna sosai don ko alheri wani yayi mata, tana fada masa ya kira ya yi godiya.
Ya ce ta taba samun matsalar gida kuma abokan sana'arta sun hada mata sama da miliyan daya.
Ali Nuhu
A yayin da BBC ta nemi jin ta bakin Ali Nuhu, ya ce bai dace ta yi musu kudin goro ba, saboda ko aiki na karshe da suka yi a fim dinsa mai suna Alaka ya biya ta dubu arba'in.
"Ka san wasu su kan yi wa mutane yadda suka ga dama, wani sai ya kyautata maka, wani kuwa ba haka ba.
"Ya dace idan mutum na bayani ya dinga tantancewa ya sanar da wasu na kyautata masa kuma ya bayyana wasu basu yi masa," in ji Sarki Ali Nuhu.
Jarumin ya ce kalamanta sun ja masa zagi saboda fina-finan ta na kwanakin nan duk da shi suka yi. Ya ce ko kadan bai ga laifin masu kallo da ke zaginsa ba, saboda ba su san komai a kai ba.
Asali: Legit.ng