Da Dumi-Dumi: Zamu kawo karshen Bokon Haram kafin wa'adin Buhari ya kare a 2023, Zulum
- Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya ce da ikon Allah kafin Buhari ya miƙa nulki a 2023 za'a kawo karshen Boko Haram
- Gwamnan ya ce ya gana da Buhari ne game da karuwar miƙa wuyan yan ta'adda a Borno da kuma lamarin yan gudun hijira
- A cewarsa karfin soji kaɗai ba zai magance matsalar ba, dan haka yake ganin ya dace a yi amfani da maslahar siyasa
Abuja - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya bayyana kwarin guiwarsa cewa matsalar yan ta'addan Boko Haram zata kare kafin shugaba Buhari ya miƙa mulki a 2023.
The Nation ta rahoto cewa Zulum ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati, bayan gana wa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Aso Villa.
Gwamnan ya sanar da cewa akalla yan ta'adda 30,000 daga ƙungiyar Boko Haram da yar uwarta ISWAP ne suka miƙa wuya ga gwamnatin Najeriya zuwa yanzun.
Haka nan kuma Zulum ya tabbatar da cewa gwamnatin jahar Borno ba ta sanya wa yan ta'adda wata garabasa domin sun miƙa wuya ba, inda ya jaddada cewa suna miƙa wuya ne bisa ratsin kansu.
Ko me gwamnan ya zanta da shugaba Buhari?
Gwamna Zulum ya ce ya tattauna da shugaban ƙasa Buhari game da cigaba da miƙa wuyan yan ta'adda da kuma lamarin da ya shafi yan gudun hijira.
Zulum yace:
"Mun tattauna da shugaba Buhari kan yanayin da ake ciki a gabashin Borno, kuma muna aiki tukuru wajen kawo karshen ta'addanci kafin wa'adin mu ya kare a 2023."
Bugu da kari, Zulum ya tabbatar da cewa jihar Borno ta samu tsaro a yanzun idan akayi la'akari da yadda matsalar take a can baya.
Daga nan kuma gwamna Zulum ya yi fatan cewa idan Allah ya so za'a cigaba da samun zaman lafiya har komai ya zo ƙarshe.
A cewar Zulum matakan karfin soji kaɗai ba zai kawo ƙarshen yakin ba, dan haka ya dace a yi amfani da maslahar siyasa wajen kawo ƙarshen lamarin. kamar yadda Vanguard ta rahoto.
A wani labarin na daban kuma Jiragen yakin Najeriya sun yi ruwan wuta kan kwamandojin yan bindiga da yaransu 37 a jihar Neja
Bayan yanayi ya gyaru a sama, jiragen yakin rundunar sojin Najeriya sun yi luguden wuta kan yan bindiga a jihar Neja.
Rahoto ya nuna cewa Dakarun sojin ƙasa sun marawa jiragen baya har aka kashe jagororin yan bindiga da yaransu 37.
Asali: Legit.ng