Ana neman N25bn, Attajiri Dahiru Mangal ya yi wa gwamnatin Yobe kyautar ban mamaki
- Alhai Dahiru Barau Mangal ya ba gwamnatin jihar Yobe gudumuwar Naira biliyan 1 yau a Abuja
- Shugaban kamfanin na Mangal Group ya yi wannan kyauta ne domin a inganta ilmin boko a Yobe
- Sauran masu kudin Najeriya da gwamnoni sun bada na su gudumuwan a taron da aka kira a yau
FCT, Abuja - Shugaban kamfanin Mangal Group, Dahiru Barau Mangal ya bada gudumuwar kudi Naira biliyan 1 ga jihar Yobe domin a bunkasa sha'anin ilmi.
Rahotannin da muka samu sun bayyana cewa Alhaji Dahiru Barau Mangal ya taimaka da wannan kudi ne domin gwamnatin Yobe ta farfado da ilmi.
News Digest ta ce Attahirin ya bada gudumuwar ne a wajen taron baran da gwamnatin jihar Yobe tayi a garin Abuja a yau Alhamis, 9 ga watan Fubrairu, 2020.
Bayan Dahiru Barau Mangal, mai kudin nahiyar Afrika. Alhaji Aliko Dangote ya bada Naira miliyan 350 yayin da kungiyar gwamnoni ta bada N350m.
Kamfanin Tahir Group of Companies sun bada na su gudumuwar na N100m a zaman da aka yi dazu.
Kokarin gwamnatin Mala Buni
Mai girma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi jawabi a wajen taron, ya kara jaddada muhimmancin maida hankali domin farfado da harkar ilmi.
Ganin bukatar hakan ne Alhaji Mai Mala Buni ya nemi mutane daga waje su taimakawa gwamnatin Yobe domin a iya tara kudi har Naira biliyan 25.
Gwamna Mala Buni ya ce za ayi amfani da kudin wajen inganta ilmi da kawo tsare-tsare da za su gyara karatun firamare da na sakandare a fadin jihar Yobe.
Har ila yau, kudin da za a tara za su yi amfani wajen kara adadin masu zuwa makaranta, kuma a rage yawan yara da ‘yan matan da ba su yin karatun boko.
Gwamnan ya ce kudin za su yi amfani wajen kawo kayan aiki da wajen daukar karatu, da samar da malamai, tare da samun hadin-gwiwar sauran kungiyoyi.
Makarantar Almajirai
A wajen wani irin wannan taro da aka yi a Yenagoa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana dalilin da ya sa ya kawo tsarin makarantun Almajirai a gwamnatinsa.
Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya ce ya yi wannan yunkuri ne domin ganin Almajirai sun hada da karatun ilmin zamani ta yadda za su samu abin auno shinkafa.
Asali: Legit.ng