An kama karamin yaro na hannun daman kasurgumin ɗan bindiga a Zamfara
- Jam'an hukumar Civil Defence reshen jihar Zamfara sun samu nasarar damke wani hatsabibin yaro da zargin ayyukan ta'addanci a jihar
- Kakakin hukumar NSCDC na jihar, Iko Oche, yace jami'ai sun kama yaron, Sani Suleiman, a yankin Gusau, babban birnin jihar
- Yace Yayin bincike Suleiman ya faɗi yadda ya samu horo a dajin Sabubu, da yadda yake wa mata fyaɗe idan aka kamo su
Zamfara - Jami'an hukumar tsaron Civil Defence, (NSCDC) reshen jihar Zamfara sun kama wani yaro ɗan shekara 14, Sani Suleiman, bisa zargin hannu a ta'addancin yan bindiga.
Wannan na ƙusnhe ne a wata sanarwa da kakakin hukumar NSCDC, Ikor Oche, ya fitar, yace Suleiman ɗan asalin ƙauyen Kadage, ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamfara.
A cewarsa, jami'an NSCDC sun samun nasarar kama yaron ne yayin da suka fita sintiri ranar 7 ga watan Fabrairu, 2022 da misalin ƙarfe 1:00 na dare a yankin Samaru, Gusau.
Oche ya ƙara da cewa jami'an sun taso ƙeyarsa zuwa Hedkwatar NSCDC ta jiha dake Gusau domin zurfafa bincike kan alaƙar yaron da ayyukan yan bindiga.
Me bincike ya gano game da karamin yaron?
Oche yace yayin gudanar da bincike sun gano cewa ƙasurgumin ɗan bindiga, Salihu, shi ya horad da karamin yaron yadda ake amfani da bindiga a dajin Sabubu.
Kakakin hukumar ya ce:
"Binciken mu ya gano cewa ɗaya daga cikin manyan shugabannin yan bindiga, Salihu, shi ya horad da yaron kan amfani da makami a dajin Sabubu. Kuma ya amsa cewa yana bada gudummuwa wajen satar dabbobi da garkuwa."
"Haka nan kuma ƙaramin yaron ya amsa laifin cewa yana yi wa mata fyaɗe idan aka sace su aka kawo su sansanin su."
"A halin yanzun muna cigaba da gudanar da bincike kuma da zaran mun kammala, jami'ai za su ɗauki matakin da ya dace."
Daga ƙarshe ya yi kira ga iyaye su ɗauki matakin kulawa da 'ya'yan su, domin kare mugayen halaye a tsakanin yara ƙanana.
A wani labarin na daban kuma Yan bindiga cikin kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa a Ogun
Yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun bindige wani hamshakin ɗan kasuwa a Gidan man fetur na jahar Ogun.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun zo a cikin kayan sojoji, suka harbe mutumin a kai, sannan suka yi gaba da wasu kuɗaɗe dake cikin motarsa.
Asali: Legit.ng