Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe 'yan ISWAP da B/H 120, sun kamo 50, sun kwato makamai
- Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kashe wasu mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram
- Dakarun Operation HADIN KAI sun kuma kashe mayakan kungiyar ISWAP
- Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko ya ce an kwato makamai da dama a aikin sojin
Dakarun rundunar sojojin Najeriya karkashin atisayen Operation HADIN KAI sun kashe mayaka 120 a cikin yan makonnin da suka gabata.
Daraktan yada labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 10 ga watan Fabrairu, a taron manema labarai wanda wakilin Legit.ng ya halarta a Abuja.
Ya ce dakarun sun kuma kama yan ta’adda 50, sannan suka kwato motocin harbi guda 5, makamai iri-iri guda 50 da kuma alburasai daban-daban guda 200 daga yan ta’addan.
Ya kara da cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Bugu da kari, dakarun sun ceto yan farar hula 25 da aka yi garkuwa da su.”
Mayakan kungiyar ta’addanci da iyalansu sun mika wuya
Hakazalika, jimlar yan ta’adda 965 da iyalansu da yara 550 ne suka mika wuya ga dakarun da aka tura wurare mabanbanta da suka hada da Gamboru, Tumbumma, Kukawa, Baga, Gwoza, Mallam Fotori, Damboa, Kirta Wulgo, Bun Yadi, Gujiba, Madiya duk a jihohin Borno da Yobe.
Onyeuko ya ce:
“Yana da kyau a lura cewa daga cikin ‘yan ta’adda 965 da suka mika wuya a lokacin da ake magana a kai 104 sun fito ne daga sansanin ISWAP inda suka mika wuya ga sojoji a Marte.
“An dauki cikakkun bayanai nay an ta’addan da suka mika wuya kuma an mika shi ga hukumomin da suka dace don daukar matakin da ya kamata.”
Mayakan ISWAP da iyalansu 104 sun mika wuya
A gefe guda, rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa Mayakan kungiyar ta’addanci na ISWAP da iyalansu 104 sun mika wuya a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, ta bayyana cewa mayakan da suka saduda sun hada da maza 22 da mata 27 da yara 55.
Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa, yan ta’addan da kansu ne suka mika wuya ga dakarun runduna ta musamman ta 25 a yankin Damboa da ke Jihar Borno.
Asali: Legit.ng