Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban kwalejin Katsina, Dr Ibrahim Abubakar Gafai, ya rasu

Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban kwalejin Katsina, Dr Ibrahim Abubakar Gafai, ya rasu

  • Mataimakin shugaban kwalejin ilimi ta tarayya ta Katsina, Dr Ibrahim Abubakar Gafai, ya riga mu gidan gaskiya
  • Dr Gafai ya kwanta dama ne a safiyar yau Alhamis, 10 ga watan Fabrairu bayan ya sha doguwar jinya
  • Ana gudanar da jana'izarsa a gidansa da ke kwatas din Gafai, bayan gidan man AP

Katsina - Labari da muke samu a yanzu haka shine cewa Allah ya yiwa mataimakin shugaban kwalejin ilimi ta tarayya ta Katsina, Dr Ibrahim Abubakar Gafai, rasuwa.

A cewar wata majiya ta iyalansa, Dr Gafai ya rasu ne a yau Alhamis, 10 ga watan Fabrairu bayan ya yi fama da dogon jinya, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban kwalejin Katsina, Dr Ibrahim Abubakar Gafai, ya rasu
Mataimakin shugaban kwalejin Katsina, Dr Ibrahim Abubakar Gafai, ya kwanta dama Hoto: Katsina Post
Asali: Facebook

A yanzu haka ana shirye-shiryen jana’izarsa a gidansa da ke kwatas din Gafai, bayan gidan man AP.

Kara karanta wannan

Tsadar mai: Man fetur lita milyan 300 ya dira Najeriya, NNPC

Shafin Katsina Post ma ta fitar da labarin mutuwar tasa a wata wallafa da tayi a shafinta na Facebook.

Ta rubuta

"Mataimakin shugaban makarantar FCE Katsina (Deputy Provost), Dr. Ibrahim Abubakar Gafai ya rasu.
"Dr. Gafai ya rasu ayau alhamis bayan yasha fama da rashin lafiya.
"Za'ayi jana'izar shi da misalin karfe 10:00am na safe a unguwar magangarin Gafai wajen gidan man AP. "

Ɗalibar 200-Level a Jami'ar Najeriya ta faɗa cikin Masai, Allah ya mata rasuwa

A wani labarin, mun ji cewa dalibar 200-Level a sashin koyon harsunan Afirka na jami'ar Obafemi Awolowo University, dake Ile Ife, Ajibola Ayomikun, ta rigamu gidan gaskiya bayan ta faɗa cikin Shadda.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Ayomikun ta faɗa Shadda ne a ɗaya daga cikin gidan kwanan ɗalibai na wajen makaranta mai suna BVER, dake Student's Village.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa uwargidar Sarkin Muradun rasuwa, Buhari ya aika sakon ta'aziyya

Kakakin jami'ar Obafemi Awolowo, Abiodun Olarewaju, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya bayyana cewa jami'a baki ɗaya ta shiga jimami da takaici kan abin da ya faru da ɗalibarta mara daɗin ji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng