Yadda na sha da kyar, aka zarge ni da yunkurin sata a London, Jarumin barkwanci Bovi
- Dan wasan barkwanci na yankin kudancin kasar nan, Bovi Ugboma, ya sanar da yadda ya sha da kyar a hannun jami'an wani otal a London
- Bovi ya ce tun a gida Najeriya matarsa ta yi amfani da katin ta wurin biya masa kudin dakin da zai sauka, amma ya na zuwa aka fara masa kallon barawo
- Dan wasan barkwancin ya sanar da yadda ya sha da kyar bayan da yace su duba google su gane ko shi waye, ba sata ya je yi ba
- Ya koka da yadda 'yan damfarar zahiri da na yanar gizo suka bata harkoki, shiyasar duniya duk aka daina yadda da jama'a
Fitaccen dan wasan barkwanci na kudu, Bovi Ugboma, ya bayar da labarin abinda ya faru da shi a wani otal da ke London inda aka kusan zarginsa da sata.
A jerin wallafar da Bovi yayi yayin da ya ke bayar da labarin a ranar Laraba, jarumin barkwancin ya bayyana yadda ya sanar da jami'an otal din da ke London da su duba 'google' game da shi yayin da aka titsiye shi.
Kamar yadda yace, ya na kokarin shiga otal din a London bayan isar sa birnin, aka bukaci ya nuna katinsa da yayi amfani da shi wurin biyan kudin dakin.
Bovi ya ce ya sanar da su cewa matarsa ce ta biya da katin ta kuma ta na Najeriya, Punch ta ruwaito.

Source: Instagram
Punch ta ruwaito cewa, ya ce bayaninsa bai saukaka lamarin ba domin sun fara tunanin sata ya je yi.
Dan wasan barkwancin ya ce lamarin ya kara cabewa yayin da katinsa ya kasa aiki.
Domin tseratar da kansa daga lamarin, Bovi ya bayyana cewa wannan ne karon farko da yace a duba shi a google.
A wallafarsa, dan wasan ya kara da kafa misali da wani dan damfara mai suna Simon Leviev, wanda aka sani da Ponzi Scheme da kuma damfarar yanar gizo.

Kara karanta wannan
Abun alherin da jarumi Ali Nuhu ya yi wa wata mai tallar awara, ya taba zukatan jama'a
Bovi ya ce Leviev ya bata ko inda da damfararsa kuma ya sa hukumomi suka bude idonsu kan masu damfara ta fili da na yanar gizo.
Dan wasan barkwancin ya ce:
"Simon Leviev ya lalata ko ina fa. Na yi kokarin shiga wani otal a Lonodon amma sai suka ce sai na gabata da katin da na yi amfani da shi na biya kudin daki.
"Na sanar da su cewa mata ta ce ta yi min kuma ta na Najeriya. Wannan abu ya sake munana lamarin. Sun fara tsammanin sata zan yi. Karin takaici kuma kati na ya ki aiki.
"A karon farko kenan na rayuwata da na ce su duba google domin gane ko ni waye."
Tirkashi: An gano zunzurutun dukiyar da Cristiano Ronaldo ke samu a duk wallafarsa ta Instagram
A wani labari na daban, fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo, mai mabiya sama da miliyan dari hudu shi ne dan Adam da jama'a suka fi bibiyar shafinsa na Instagram a duniya.
An gano cewa irin makuden kudaden da ya ke samu a duk wallafar da yayi sun kai £1.7 miliyan, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kara karanta wannan
Bawan Allah ya yi wa Hadiza Gabon zagin cin mutunci, ta yi masa martani da kyakyawar addu'a
Dan wasan kwallon kafan kungiyar kwallo ta Manchester United din ya zama wanda jama'a suka fi bibiyar shafinsa na Instagram a ranar Asabar da ta gabata, inda Kylie Jenner ke biye da shi a matsayi na biyu.
Asali: Legit.ng
