Kotu ta garkame jami'an Sibil defens biyu kan zargin laifin fashi da makami

Kotu ta garkame jami'an Sibil defens biyu kan zargin laifin fashi da makami

Legas - Wata kotun jihar Legas dake Ikeja ranar Laraba ta garkame jami'an hukumar Sibil Defens -Amarachukwu Asonta da Adebayo Ajayi, 32 kan zargin laifin fashi da makami.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewa Mai Shari'a Oyindamola Ogala ta bada umurnin garkamesu ne bayan sun musanta zargin da ake musu.

Hukumar DPP ta gwamnatin jihar Legas ce ta shigar da su kotu.

Kotu ta garkame jami'an Sibil defens biyu kan zargin laifin fashi da makami
Kotu ta garkame jami'an Sibil defens biyu kan zargin laifin fashi da makami
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar diraktan DPP, Dr Jide Martins, jami'an NSCDC sun aikata laifin ne misalin karfe 2:20 na daren 30 ga Junairu, 2018, a titin Yaya Abatan, Ogba, Legas.

Yace:

"Jami'an biyu tare da wasu da muke nema har yanzu, rike da makamai sun sace motar kwantena IVECO mai lambar - LSR746XD.

Kara karanta wannan

Baba-Saliu: 'Yan bindiga sun sace shugaban IPMAN, sun bindige direbansa har lahira

"Kwantenan na dauke da katon giyan Chelsea and Action Bitters guda 1700 wanda kudinsa ya kai N2.7 million, wasu kayayyaki, wayoyi da makudan kudi."
"Ya Alkali mai shari'a, tun 2018 ake kan karar nan. Sun dade suna gudunma kotu duk da kotu ta bada umurnin damkesu."

Ya bukaci kotu ta garkamesu a kurkuku.

Lauyan jami'an tsaron, Dapo Daramola, ya nemi kotu ta basu beli.

Amma Alkali Oyindamola Ogala ta bada umurnin garkamesu a kurkuku kuma ta dage zaman zuwa ranar 23 ga Febrairu don shawara kan belin da suka nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng