Shugaban NNPC ya bayyana wadanda suka shigo da rubabben fetur daga kasar waje
- An ji cewa an samu shigowar wani man fetur maras kyau a kasar nan wanda yake lalata na’urori
- Shugaban kamfanin mai na kasa, Malam Mele Kolo Kyari ya fito ya yi wa mutanen Najeriya bayani
- Wasu kamfanoni ne suka yi kuskuren dakon wannan rubabben mai kwanakin baya daga Belgium
Abuja - Shugaban kamfanin mai na Najeriya, Mele Kolo Kyari ya yi bayani a kan yadda man fetur maras kyau ya zo kasar nan ba tare da an gane ba.
A ranar Laraba, 9 ga watan Fubrairu 2022, gidan talabijin na Channels TV ta rahoto Mele Kolo Kyari yana cewa man ya shigo ne daga kasar Belgium.
Ganin halin da aka shiga na wahalar man fetur a yankunan Abuja da Legas, hakan ta sa dole Kyari ya fito ya yi wa al’umma bayanin abin da ya faru.
“Ya kamata a fahimci cewa ba a yin gwajin nauyin sinadarin Methanol da ke cikin fetur a lokacin da mai ya shigo Najeriya, don haka ba a gane ba.”
- Mele Kolo Kyari
Rahoton ya ce Mele Kolo Kyari bai iya bayyana lokacin da aka shigo da wannan mai ba, amma ya ce an gano hakan ne a karshen watan Junairun jiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“A ranar 20 na Junairu 2020, NNPC ta samu rahoto daga jami’anmu cewa akwai tsabbi-tsabbi a jiragen man da aka kowa Najeriya daga Antwerp-Belgium.
“Kamfanin NNPC ta gudanar da bincike, ta gano akwai sinadaran Methanol a cikin jiragen ruwa na mai hudu da aka shigo da su.” - Mele Kolo Kyari
Kamfanonin da suka yi dakon wannan mai da ya gurbace a jiragen ruwansu su ne; MRS, Emadeb/Hyde/AY Maikifi/Brittania-U Consortium.
Shugaban kamfanin na NNPC ya ce kamfanonin Oando da Duke Oil sun samu wannan matsala.
An ba jiragen satifiket kamar yadda ya kamata bayan sun shigo da wannan mai daga kasar Turan bayan an yi gwaje-gwajen GMO, SGS, GeoChem da na G&G.
Sai daga baya ne ya bayyana cewa an samu methanol fiye da kima a cikin man fetur din.
Wadanda suka shigo da fetur mai methanol
1 MRS MT Bow Pioneer LITASCO Terminal, Antwerp-Belgium
2 Emadeb/Hyde/AY Maikifi/Brittania-U Consortium MT Tom Hilde
3 Oando MT Elka Apollon
4 Duke Oil MT Nord Gainer
Asali: Legit.ng