Da Dumi-Dumi: Ɗalibar 200-Level a Jami'ar Najeriya ta faɗa cikin Masai, Allah ya mata rasuwa
- Wata ɗaliba a jami'ar Obafemi Awolowo dake shekara ta biyu a karatu, Ajibola Ayomikun, ta faɗa cikin shadda kuma ta mutu
- Mai magana da yawun jami'ar OAU, Abiodun Olarewaju, yace an yi kokarin kai mata agaji, amma ana isa Asibiti rai ya yi halinsa
- VC na jami'ar Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya yi alƙawarin gudanar da bincike da hukunta duk mai hannu a lamarin
Ɗalibar 200-Level a sashin koyon harsunan Afirka na jami'ar Obafemi Awolowo University, dake Ile Ife, Ajibola Ayomikun, ta rigamu gidan gaskiya bayan ta faɗa cikin Shadda.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Ayomikun ta faɗa Shadda ne a ɗaya daga cikin gidan kwanan ɗalibai na wajen makaranta mai suna BVER, dake Student's Village.
Kakakin jami'ar Obafemi Awolowo, Abiodun Olarewaju, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Ya bayyana cewa jami'a baki ɗaya ta shiga jimami da takaici kan abin da ya faru da ɗalibarta mara daɗin ji.
The Cable ta rahoto ya ce:
"Lokacin da muka samu labari, nan take muka haɗa tawagar taimakon gaggawa a jami'a, jihar Osun da kuma Asibitin koyarwa, wanda suka yi namijin kokari har suka fito da ita."
"Ba tare da ɓata lokaci ba aka tafi da ita Asibitin koyarwa na jami'ar OAU, inda aka tabbatar da rai ya yi halinsa."
Wane mataki jami'a ta ɗauka?
Mataimakin shugaban jami'ar (VC), Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya jajantawa sauran ɗalibai yayin da ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamaciyar.
VC, wanda ya bayyana lamarin da ba za'a amince ba, ya sha alwashin gudanar da bincike kan musabbabin da ya jawo mutuwar ɗalibar kuma a ɗauki mataki kan duk wanda aka gano yana da hannu.
Ogunbodede ya bukaci ɗalibai su kwantar da hankulan su kuma su bi doka sau da kafa yayin da jami'an yan sanda suka shiga lamarin domin gudanar da bincike.
A wani labarin kuma Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya jihar Kano, ta yi jawabi mai ratsa zuciya
Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari ta kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Sheikh Ahmad Bamba da Hanifa Abubakar.
Aisha Buhari ta yi bayani mai ratsa zuciya game da Hanifa, inda tace ita ma uwa ce kuma tana da jikoki a makarantar Firamare.
Asali: Legit.ng