Gwamna ya dakatar da hadiminsa saboda ƙin raba wa mutane kayan agaji har suka lalace

Gwamna ya dakatar da hadiminsa saboda ƙin raba wa mutane kayan agaji har suka lalace

  • Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi ya dakatar da Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Jihar Ebonyi, Mr Ozioma Eze
  • An dakatar da Ozioma Eze ne saboda sakaci da aikinsa ta inda ya bari wasu kayayyakin agaji suka lalace ba tare da an raba wa al'umma ba
  • Gwamnan ya umurci Eze ya mika dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsa ga Kwamishinan Raya Al'umma da Saka Idanu

Ebonyi - Gwamnan Jihar Ebonyi David Umahi ya bada umurnin dakatar da Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Jihar Ebonyi, Mr Ozioma Eze ba tare da bata lokacin ba, rahoton The Sun.

Sanarwar ta sakataren gwamnatin jihar, Dr Kenneth Ugbala ya fitar ta ce an dakatar da Mr Ozioma ne saboda sakaci da aiki da ta janyo wasu kayayyakin agaji da ya kamata a raba wa mutane suka lalace.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Mun fara shawara kan mikawa gwamnatin Amurka Abba Kyari

Gwamna ya dakatar da hadiminsa saboda ƙin raba wa mutane kayan agaji har suka lalace
Gwamna Umahi ya dakatar da hadiminsa saboda kin raba wa al'umma kayan agaji. Hoto: Vangaurd
Source: Twitter

An Umurci Eze ya mika kayan gwamnati da ke hannunsa kafin a tashi aiki

Gwamnan ya bada umurnin Eze ya mika dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsa zuwa ga Kwamishinan Raya Al'umma da Saka Idanu kafin a tashi aiki a ranar Laraba, The Sun ta ruwaito.

"An umurci Fasto Ozioma Eze ya mika dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsa zuwa ga Kwamishinan Raya Al'umma da Saka Idanu kan ayyuka kafin a tashi aiki a ranar Laraba 9 ga watan Fabrairun 2022.
"A tabbatar an bi umurnin sau da kafa," a cewar sanarwar.

Sanarwar ba ta kayyade tsawon lokacin dakatarwa ba.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164