Mabiya sun dauke kafa daga ofishin mataimakin Gwamnan Zamfara yayinda ake shirin tsigeshi
- Majalisar jihar Zamfara na cigaba da shirye-shiryen tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahadi Aliyu Gusau
- Bayan da aka yi ta dambarwa kan batun tsige mataimakin gwamnan, ya garzaya kotu domin kare kansa
- Mabiya sun dauke kafa daga ofishinsa tun bayan sanarwar majalisa na shirin tsigeshi
Gusau - Mutane sun dauke kafa daga ofishin mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Muhammad, biyo bayan shirin tsigeshi da majalisar dokokin jihar ke yi.
Mahdi Aliyu, wanda 'da ne ga tsohon Ministan tsaro, Janar Aliyu Gusau, sun yi hannun riga da maigidansa, Gwamna Bello Matawalle, sakamakon rashin sauya sheka tare da gwamnan zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta ruwaito tun bayan sauya shekan Gwamna Matawalle mataimakinsa Mahdi Gusau ya rage zuwa ofishinsa.
Majiyoyi sun bayyana cewa tuni mataimakin gwamnan ya daina zuwa ofis.
A cewar majiyoyi,
"Hakane, mataimakin Gwamnan na sane da dukkan abubuwan da suke faruwa kuma na san hukuncin kotu na watsi da karar da aka shigar kan sauya shekar gwamnan na daya daga cikin abubuwan da ke karfafa musu gwiwan son tsigeshi."
Majalisa ta lissafo laifukan Aliyu Gusau
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta aikewa mataimakin gwamnan jihar Mahadi Ali takardar tsige shi.
Majalisar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shamsudeen Basko, shugaban kwamitin riko na majalisar, yanzu haka ta tattauna da mataimakin gwamnan ta hannun sakataren gwamnatin jihar.
A cikin sanarwar, Mista Basko ya ce ana zargin mataimakin gwamnan ne da laifin yin amfani da mukaminsa, da wadata kansa da aikata laifuka ta hanyar amfani da kudaden jama'a da kuma gazawa wajen gudanar da ayyukan gwamnati.
Ya ce:
“Amfani da ofishinsa. Wannan ya hada da saba wa kundin tsarin mulki sashe na 190 da na 193 (1), (2) (a) (b) (c), na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya 1999 (wanda aka yi masa kwaskwarima).
“Masu aikata laifuka ta hanyar amfani da kudaden jama’a; ya hada da karkatar da kudaden gwamnati da aikata laifuka, da hada baki da zamba a jihar da kuma amincewa da yin murabus na rashin tabbas a ofishinsa.
"Rashin sauke ayyukan tsarin mulki wanda ke haifar da rashin biyayya."
Asali: Legit.ng