Hotunan dagargazar da sojin Najeriya suka yi wa EJIKE, fitaccen dan awaren IPOB/ESN da yaransa 3
- Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar sheke Ejike, wani shugaban 'yan awaren IPOB/ESN tare da mukarrabansa 3 a Ihiala
- An kira sojojin ne cike da damuwa kan yadda Ejike da yaransa suke ta ruwan wuta ga duk wanda ya fito bayan kungiyar ta saka dokar hana fita
- Daga zuwan dakarun, Ejike da yaransa suka bude musu wuta, zakakuran sojojin sun halaka shi tare da samun miyagun makamai a tare da su
Anambra - Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar halaka gagararrun 'yan awaren IPOB/ESN a garin Ihiala da ke jihar Anambra.
'Yan bindigan da suka tsaya tsayin daka wurin tirsasa jama'a su zauna gida dole suna ta ruwan harsasai ne a kusa da wata gidan mai da ke garin Ihiala.
Bayan da dakarun sojin Najeriya suka samu kiran gaggawa, sun gaggauta zuwa wurin domin kwantar da tarzomar. Daga zuwansu kuwa, 'yan bindigan suka bude musu wuta amma zakakuran sojin sun halaka shugabansu Ejike da wasu mutum uku.
Abubuwan da aka samo daga miyagun yayin arangamar sun hada da babur daya, bindigogi biyu, harsasai masu rai guda 12 da kuma wani abu da ake zargin wiwi ne da sauransu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Cike da takaici, hatsari ya ritsa da wata mota daya ta yaki da ke dauke da dakarun soji sakamakon matsalar da ta samu a titi.
Hafsan soja daya da wani soja sun rasa rayukansu a yayin hatsarin yayin da wasu biyu suka samu rauni. A halin yanzu masu raunin suna asibitin sojoji inda ake kula da su.
Kamar yadda takardar da Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a Facebook ta ce, suna fatan gafarar Ubangiji ga mamatan.
Ya yi kira ga jama'a da su cigaba da bai wa sojojin hadin kai da sauran jami'an tsaro ta hanyar samar da bayanai a kan lokaci wanda zai bayar da damar samar da salama da daidaituwa a yankin.
Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30
A wani labari na daban, an zargi wasu daga cikin mambobin IPOB da hallaka wani makiyayi a kwanan nan yayin da al'amarin ya jefa iyalansa, uban gidan sa dan kabilar Ibo da wadanda suka san shi cikin alhini.
Makiyayin, Muhammad Alarabe alias Ogbodo, ya kai kimanin shekaru 20 ya na kula da shanu, dan kabilar Ibo kafin harbe shi da aka yi a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu, 2022.
Hakazalika, maharan sun sheke wasu daga cikin shanun uban gidan Alarabe, Chief Oeter Chukwuani Onyeabor, fitaccen mai sayar da shanu a jihar Enugu, wanda ya gaji kasuwancin daga marigayin mahaifinsa.
Asali: Legit.ng