Yanzu-yanzu: FG ta tabbatar da cewa an samu matsala, an sayarwa gidajen mai gurbataccen fetur
- Gwamnatin tarayya ta tabatar da cewa an samu gurbatattun man fetur a gidajen mai a fadin tarayya
- Wannan ya biyo bayan bidiyoyin da suka yadu a kafafen sada zumunta tun lokacin da aka ga wani gidan mai yana matsa gurbataccen mai ga kwastoma
- Gwamnati ta ce tana kokarin takaita siyar wannan gurbataccen mai na kimanin lita milyan 80
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar lura man feturin saman kasa NMDPR ta tabbatar da cewa an samu matsala wajen sarrafa man feturin da aka sayarwa gidajen mai.
Hukumar NMDPR ta bayyana hakan ranar Talata inda tace adadi sinadarin 'Methanol' dake cikin feturin ya yi yawa.
A jawabin da ta saki, ta bayyana cewa an gano dan kasuwan man da yake raba wannan mai kuma za'a hukuntasa yadda ya kamata.
Hukumar tace:
"An gano man feturin mai sinadarin Methanol fiye da yadda ya kamata a gidajen mai a Najeriya."
"Methanol wani sinadari ne da ake karawa fetur don daidaita shi."
"Domin tabbatar da lafiyar motoci, an kwashe wannan gurbataccen man daga cikin jama'a, ciki har da tankunan man dake hanya yanzu haka."
An gano dan kasuwan dake sayar da gurbataccen man
Hukumar ta kara da cewa ta gano inda gurbataccen man ya fito kuma an dakile.
Hakazalika hukumar tace za'a dau matakan da ya kamata kan dan kasuwan,
Jawabin yace:
"An gano mai fitar da mankuma hukumar da NNPC zasu dau mataki. An umurci NNPC da dukkan kamfanonin mai su tabbatar da akwai isasshen mai a gidajen man fadin tarayya."
Tsadar mai: Bidiyo ya fallasa yadda ake sayar da gurbataccen mai a wani gidan mai
Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa ta kowane bangare, wasu masu gidajen mai suna kara wa ciwon gishiri ta hanyar sayar da gurbataccen mai.
Wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya bayyana lokacin da wani ma'aikacin gidan mai ke kokarin cika wata gorar ruwa da wani mai launin ja da ya yi kama da gurbatacce.
A bidiyon da Legit.ng Hausa ta samo a kan shafin Facebook na jaridar Punch, an ga man da ake dura wa gorar da launin da bai yi kama da na man fetur ko kalanzir ko gas ba, duk da cewa a gidan mai ne.
Asali: Legit.ng