Malami: Akwai yuwuwar FG ta hukunta Igboho a Najeriya bayan Cotonou ta sake shi
- Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami, ya ce akwai yuwuwar gwamnatin tarayya ta ladabtar da Igboho bayan ya dawo gida
- A cewar ministan shari'ar, a halin yanzu babu abinda gwamnatin za ta iya na ceto Igboho, saboda dokar kasar ketare ya taka
- Amma kuma Malami ya tabbatar da cewa, ta yuwu a shawo kan matsalar Igboho a siyasance bayan ya dawo gida Najeriya
Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce akwai yuwuwar gwamnatin tarayya ta hukunta Sunday Adeyemo, dan aware kasar Yarabawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, a Najeriya bayan an sako shi daga jamhuriyar Benin.
A watan Yulin 2021, an kama Igboho a filin sauka da tashin jiragen sama na Cardinal Bernardino da ke Cotonou kan zarginsa da mallakar fasfotin bogi.

Source: UGC
Kwanaki kadan bayan kama shi a jamhuriyar Benin, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta na nemansa idanu rufe.
Tun bayan nan, ya kasance garkame a gidan yarin kasar, ThecCable ta ruwaito hakan.
A ranar Lahadi, Yomi Alliyu, lauyan dan awaren, ya ce gwamnatin jamhuriyar Benin ta tsawaita zaman Igbhoho a gidan yarin da wata shida.
A yayin zantawa kan lamarin, Malami a wata tattaunawar sa yayin da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta tsoma baki a lamurran dan aware ba a jamhuriyar Benin tunda zarginsa ake da take dokar kasar.
"Al'amari ne da ya shafi hukunta shi a kasar waje, kuma abu bayyananne shi ne an garkame shi saboda take dokar wata kasa. A saboda hakan, hukunta shi suke yi," yace.
Da aka tambaya ko ana kokarin dawo da Sunday Igboho gida Najeriya, antoni janar din ya ce gwamnatin tarayya za ta bai wa Jamhuriyar Benin damar hukunta shi.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Jamhuriyar Benin ta yanke sake tsare Sunday Igboho na tsawon watanni
"Za mu bar dokar kasar ta yi aiki a kansa kuma bayan ya dawo gida zai fuskanci hukuncin dokar kasar Najeriya da ya take," ya kara da cewa.
"Matsayar mu a yanzu shi ne, ba za mu saka baki a hukuncin da ake masa a kasar ketare ba, duba da cewa dokar su ya taka."
Da aka tambaya ko akwai hanyar shawo kan matsalar a siyasance, Malami ya ce babu wani hanyar shawo kan lamarin a siyasance tunda mai rajin kare hakkin dan Adam din na fuskantar shari'a ne a kasar ketare.
Ya ce akwai yuwuwar a duba hanyar shawo kan matsalar a siyasance idan ya dawo gida Najeriya.
Tura ta kai bango: Za mu yi amfani da 'tsafi' mu fito da Sunday Igboho daga gidan yari, Ƙungiyar Agbekoya
A wani labari na daban, kungiyar manoma ta Agbekoya a Najeriya ta bayyana cewa za ta yi amfani da 'tsafi' ta ceto mai rajin kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo aka Sunday Igboho idan gwamnatin Jamhuriyar Benin ta cigaba da tsare shi ba bisa ka'ida ba.
Kamorudeen Okikiola, shugaban kungiyar ya ce Igboho ba mai laifi bane, amma mai neman 'yanci ne da aka tsare shi ba bisa ka'ida ba da hadin bakin gwamnatin Najeriya, rahoton Vanguard ta ruwaito.
Ya yi wannan jawabin ne yayin wata tattaki na zaman lafiya da aka yi a Osogbo, babban birnin Jihar Osun a ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng

