Kwankwaso, Bugaje, jiga-jigai 14, zasu kafa sabuwar jam'iyya karshen watan nan
- Yadda siyasar 2023 zata kasance ya dau sabon salon yayinda wasu ke shirin kafa sabuwar jam'iyya
- Wasu Farfesosi da shugabannin jam'iyya na son kafa jam'iyyar da zatayi fito-na-fito na jam'iyyun PDP da APC
- Har ila yau, masu neman kujerun siyasa daban-daban sun fara bayyyana ra'ayoyinsu
Legas- Wasu jiga-jigan siyasa daga jam'iyyu daban-daban da kungiyoyi zasu kaddamar da sabuwar jam'iyyar siyasa a mako mai zuwa, rahoton Vanguard.
Wadanda ake sa ran zasu kafa wannan sabuwar tafiya sun hada da:
1. Prof Pat Utomi
2. Dr Usman Bugaje
3. Engr Musa Rabiu Kwakwanso,
4. Farfesa Kingsley Moghalu,
5. Sanata Saidu Dansadau, (Shugaban, NRM);
6. Chief Raph Okey Nwosu (Shugaban , ADC);
7. Hadjia Najatu Mohammed,
8. Prof Remi Sonaiya,
9.Pastor Ituah Ighodalo,
10. Prof Osita Ogbu;
11. Dr Sadiq Gombe;
12. Comrade Promise Adewusi;
13. Chief Akin Braithwaite;
14. Arc Ezekiel Nya Etok;
15. Lady Khadija Okunnu-Lamidi;
16. Comrade Olawale Okunniyi dss.
Yan siyasan sun yanke wannan shawara ne a taron samar da sabuwar jam'iyyar da zatayi fito-na-fito na jam'iyyun PDP da APC ranar Lahadi a Legas.
Bayan taron, yan siyasan sun saki jawabin cewa sun kafa kwamiti na musamman domin cimma wannan manufa.
Jam'iyyu da kungiyoyin da suka hallara sun hada da Rescue Nigeria Project, RNP; Nigeria Intervention Movement, ÑIM; Strategic Elements of the Civil Society Movement; Youths’ EndSars Movement, National Rescue Movement, NRM; da African Democratic Congress, ADC.
Yan bangaren Osinbajo sun tuntubi Kwankwaso
Hakazalika an tattaro cewa wasu yan bangaren mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sun tuntubi Kwakwaso, duk da cewa Osinbajo bai bayyana niyyarsa ba tukun.
Wata majiya mai karfi tace har Shugaban jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya yi kira ga Kwankwaso ya koma APC.
A cewar majiyar:
"Tattaunawa na gudana tsakanin Oga da su. Suna son ya dawo APC amma ana shawara kai. Ba a yanke ba."
Asali: Legit.ng