Wata Sabuwa: Gwamnan PDP ya fusata, ya sallami kwamishinoninsa biyu daga aiki

Wata Sabuwa: Gwamnan PDP ya fusata, ya sallami kwamishinoninsa biyu daga aiki

  • Gwamnan jihar Taraba dake arewa ta tsakiya a Najeriya ya sallami Kwamishinoninsa guda biyu daga bakim aiki
  • Gwamna Darius Ishaku ya tabbatar da haka a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa ya fitar, ya ce korar zata fara aiki nan take
  • Ɗaya daga cikin waɗan da lamarin sallamar ya shafa, Kwamishinan labarai ya tabbatar da haka, ya ce tuni ya bar ofishinsa

Taraba - Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba, ya amince da sallamar kwamishinoni biyu daga bakin aikin su ranar Litinin, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Waɗan da lamarin ya shafa sune; Kwamishinan labarai da wayar da kai, Barista Danjuma Adamu, da kuma kwamishinan cinikayya, kasuwanci da masana'antu, Yusuf Njeke.

Sakataren watsa labarai na gwamnan, Iliya Bekyu, wanda ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar, yace sallamar mutanen ta fara aiki nan take, kamar yadda Channels tv ta rauwaito

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Mun fara shawara kan mikawa gwamnatin Amurka Abba Kyari

Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba
Wata Sabuwa: Gwamnan PDP ya fusata, ya sallami kwamishinoninsa biyu daga aiki Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Bugu da ƙari, gwamnan ya umarci kwamishinan kimiyya da fasaha, Alhaji Hamana Gasol, ya kula da ma'aikatar labarai da wayar da kai.

Kazalika ya miƙa ragamar kula da ma'aikatar cinikayya, kasuwanci da masana'antu ga kwamishinan rage radadin talauci, Honorabul Jethro Yakubu Zikenyu.

Ko ya waɗan da gwamna ya sallama suka ji da lamarin?

A na shi ɓangaren, tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Taraba, Barista Danjuma Adamu, ya tabbatar da batun sallamarsa daga bakin aiki ga manema labarai.

Da yake zantawa da manema labarai ta wayar salula, tsohon kwamishinan ya ce:

"Eh tabbas gwamna ya sallame ni daga bakin aiki, labarin da kuka ji gaskiya ne, al'amura na a yanzun sun tashi daga ofishin kwamishina."

Jihar Taraba ta shiga rikicin siyasa a yan kwanakin nan, tun bayan sauya sheƙar mataimakin shugaban marasa rinjaye na majlaisar dattawan Najeriya, wanda ya fito daga jihar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun kubutar da wadanda aka sace

A wani labarin na daban kuma shugabannin majalisar dokoki biyu da wasu yan majalisu uku za su koma APC a Taraba

Da yuwuwar sauya shekar Sanata Emmanuel Bwacha zuwa APC ya zama babban alheri a siyasar jam'iyyar reshen jihar Taraba.

Tsofaffin shugabannin majalisar dokokin Taraba biyu da kuma wasu yan majalisu uku na shirin sauya sheka zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262