Cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote ya samu N217.5bn, ya tsallake biloniyoyi 6 na duniya a jerin masu arziki

Cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote ya samu N217.5bn, ya tsallake biloniyoyi 6 na duniya a jerin masu arziki

  • Aliko Dangote ya tsallake manyan biloniyoyi shida na jerin hamshakan masu kudin duniya kamar yadda Bloomberg ta bibiya
  • Sauyawar matsayin Dangote a jerin masu arziki na duniya ya zo ne bayan kari da habakar da ya ke samu a dukiyarsa cikin kwanaki 26 na farkon 2022
  • Babu shakka arzikin bakar fatan da ya fi kowa kudi a duniya ya na karuwa ne sakamakon hauhawar hannayen jarin kamfaninsa na siminti

Aliko Dangote, hamshakin mai arziki kuma wanda ya fi kowa kudi a Afrika ya samu karin N217.5 biliyan a dunkiyarsa cikin sa'o'i 8 kacal inda ya zama mutum na 91 mafi arziki a duniya.

Kamar yadda Bloomberg ta bayyana, Dangote a halin yanzu arzikinsa ya kai $20.1 wanda ya kai kashi 5.23 na ma'adanar Najeriya ta kasashen ketare mai jimillar kudi har $40.1 biliyan.

Kara karanta wannan

2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero

Cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote ya samu N217.5bn, ya tsallake biloniyoyi 6 na duniya a jerin masu arziki
Cikin sa'o'i 8 kacal, Dangote ya samu N217.5bn, ya tsallake biloniyoyi 6 na duniya a jerin masu arziki. Hoto daga NGX
Asali: Facebook

Hauhawar farashin hannun jari a kamfanin simintin Dangote, karuwar kudin mai da kuma farashin taki ya taimaki dan kasuwan Najeriyan mai shekaru 64 a duniya.

Karuwar hannun jari a kamfanin Dangote

Hamshakin mai arzikin shi ke juya dukkan kamfanonin Dangote, kamar yadda Bloomberg ta wallafa, amma da yawa daga arzikinsa na zuwa ne daga kamfaninsa na siminti wanda ya kasance mafi shaharar kamfanin siminti a Afrika.

Hannayen jarin kamfanin Dangote a sa'o'i takwas ya karu daga kashi 5.45 % zuwa N274.8.

Dangote ya mallaki kamfanin abinci na sikari, gishiri, mai, taki da sauransu tare da wasu manyan gine-gine da ake amfani da su na kasuwanci a Legas.

Dukiyar Aliko Dangote ta karu da sama da Naira biliyan 800 cikin watanni 3 a 2021

Kara karanta wannan

Layin dogon Kaduna-Kano: Da yiwuwan mu gaza kammalawa saboda rashin kudi, Amaechi

A wani labari na daban, jaridar kasar Afrika ta kudu, Business Africa Insider tace dukiyar Alhaji Aliko Dangote ta karu sosai a karshen wannan shekarar. Jaridar tace mai kudin na Afrika ya hankada gaba a jerin attajiran Duniya kamar yadda sababbin alkaluman Bloomberg Billionaires Index suka nuna.

Aliko Dangote ya yi gaba a rukunin masu kudin, inda yanzu ya kai matsayi na 102 a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar nan, Dangote ne na 118.

Business Africa Insider tace Dangote ya kara kimanin Dala biliyan biyu a dukiyarsa daga Agustan shekarar 2021 zuwa ranar 8 ga watan Nuwamban nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng