Da duminsa: Kotu ta yanke wa Jaruma Sadiya Haruna hukuncin wata 6 a gidan yari
- Wata kotun majistare da ke sama a filin jirgin sama na Kano ta yanke wa Jaruma Sadiya Haruna hukuncin zaman watanni shida a gidan yari
- Alkali Muntari Garba Dandago ya yanke mata wannan hukuncin ne kan kalaman batanci da cin zarafi da ta dinga yi a kan mawaki kuma jarumi Isah A. Isah
- A shekaru biyu da suka gabata ne hargitsi ya rincabe tsakanin Sadiya Haruna da Isah wanda tsohon saurayin ta ne, ta ce sun yi auren mutu'a
Kano - Kotu ta yanke wa jarumar Kannywood kuma mai siyar da kayan mata da maza, mai suna Sadiya Haruna hukuncin zaman wata shida a gidan yari ba tare da zabin tara ba.
An samu Sadiyan da laifin bata sunan wani jarumi kuma mawakin kannywood mai suna Isa A Isa, Sahelian Times ta ruwaito.
A wani bidiyo da ya yadu, an ga jarumar ta na kiran Isa da dan luwadi, Shege kuma manemin matan da ba zai taba tuba ba. Ta kuma zargi jarumin da neman ta da lalata ta baya.
Wata kotun majistare da ke zama a filin jirgin sama ce ta yanke wa jarumar daurin watanni shida babu zabin tara, Freedom Radio ta ruwaito.
A zaman da kotun ta yi na yau Litinin, Mai shari'a Muntari Garba Dandago ya yanke wannan hukuncin kan kalaman batancin da ta yi ga jarumi Isah I. Isah a Instagram
Idan masu bibiyar mu za su tuna, a shekarar 2019 ne aka samu hargitsi tsakanin Sadiya da Isah.
Bata yi kasa a guiwa ba ta dinga wallafa kausasan kalami a kan jarumin kuma ta dinga nadar bidiyoyinsu ta na sanya wa a shafukan sada zumunta.
Kano: Sadiya Haruna ta sha da kyar hannun Ƴan daba, sun yi yunƙurin watsa mata acid
A wani labari na daban, fitacciyar jaruma, Sayyada Sadiya Haruna, ta saki wani bidiyo inda ta koka kan wasu 'yan daba a birnin Kano sun yi yunkurin watsa mata acid a fuska a ranar Juma'a, 28 ga watan Janairu.
Cike da tashin hankali yayin da ta ke kuka tare da ihu ta yi bidiyon a cikin mota, inda wani matashi wanda ta kira da Besty ya ke jan ta.
A cewar Sadiya Haruna kamar yadda ta wallafa a shafin ta na Instagram, ta taso daga shagon ta inda ta ce wa kanin ta za ta biya kanti domin siyayya, shi ya karasa gida kafin ta iso.
Asali: Legit.ng