Buhari ya nufo gida Najeriya bayan kammala taron kungiyar gamayyar kasashen Afrika
1 - tsawon mintuna
- Shugaba Muhammadu Buhari ya juyo inda zai dawo babban birnin tarayyar Najeriya da ke Abuja bayan kwanaki da yayi a Addis Ababa
- Shugaban kasar Najeriyan ya halarci taron gwamnatocin kasashen da ke karkashin kungiyar gamayyar Afrika
- A gagarumin taron da shugabannin kasashen Afrika suka halarta, an tattauna muhimman al'amura da suka shafi siyasa da tsaro a nahiyar Afrika
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya garzayo tare da nufo gida Najeriya bayan halartar taron shugabannin gwamnatoci na kungiyar gamayyar kasashen Afrika da aka yi a birnin Adiis Ababa na kasar Ethiopia.
Kamar yadda hadimin shugaban kasan, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban Buhari ya nufo Abuja bayan kammala taron.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng
Tags: