Wata sabuwa: Jamhuriyar Benin ta yanke sake tsare Sunday Igboho na tsawon watanni
- Da alamu Sunday Igboho ya sake shiga matsala yayin da jamhuriyar Benin ta sake ba da umarnin ci gaba da tsare shi
- Wannan na zuwa kwanaki kadan bayan da wani lauya ya bayyana yiyuwar sako Sunday Igboho nan kusa
- Sunda Igboho, dan arewan Yarbawa na cikin wadanda gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo domin gurfanar dashi a gaban kotu
Sabanin rade-radin da wani lauya mazaunin Abuja, Pelumi Olajengbesi, ya yada a karshen mako na cewa nan ba da jimawa ba za a sako dan awaren Yarbawa Sunday Igboho, gwamnatin Jamhuriyar Benin ta sake sabunta tsare shi a gidan yari na wata shida.
Sabuntawar ta zo ne kasa da kwanaki biyu bayan da Olajengbesi ya bayyana hakan duk da cewa tun a lokacin ya yi murabus daga tawagar lauyoyin da ke kula da shari’ar Igboho, inji rahoton Tribune.
Olajengbesi a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya rubuta cewa:
"Cif Sunday Igboho zai fita nan ba da jimawa ba kuma za a yi gagarumin murna a fadin kasar Yarbawa.
"Babu shakka shi mutum ne mai karfin hali. Yana da muhimmanci sosai a ga shugabannin mu na Yarbawa sun daina son kai sun bar alheri ya wanzu."
Sunday Igboho zai sake watanni shida a jamhuriyar Benin
Sai dai lauyan Igboho, Cif Yomi Alliyu (SAN), a daren Lahadi ya bayyana cewa gwamnatin jamhuriyar Benin ta sabunta zamansa a gidan yari ba tare da an saurari karar ba.
Aliyu ya bayyana cewa:
"Gwamnatin Benin ta sake sabunta tsare Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho Oosa a gidan yari na tsawon watanni shida duk da cewa babu wani laifi a cikin fayil dinsu a Cotonou kuma ba tare da neman a mika shi Najeriya ba."
Tura ta kai bango: Za mu yi amfani da 'tsafi' mu fito da Sunday Igboho daga gidan yari, Ƙungiyar Agbekoya
Wannan ci gaban dai wani rauni ne da baraka ga magoya bayansa biyo bayan sanarwar Olajengbesi yayin da suke nuna damuwa kan tsawaita zamansa a gidan yari.
Igboho yana tsare a Jamhuriyar Benin tun bayan da jami'an tsaron kasar da ke nahiyar Afirka ta Yamma suka kama shi a filin jirgin saman Cotonou a lokacin da yake kokarin shillawa Jamus a watan Yulin 2021.
Igboho mai shekaru 49 da haihuwa ya bar Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin bayan da gwamnatin tarayya ta ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
Daga tserewa gwamantin Najeriya ne kuma tun daga nan ya shafe sama da kwanaki 200 a tsare a gidan yari na Jamhuriyar Benin, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Wata kotu a Benin ta hana yunkurin mika Igboho zuwa Najeriya yayin da ta yanke hukuncin a tsare dan awaren a gidan yari har domin ci gaba da sauraren karar.
Lauyan Sunday Igboho ya zare hannunsa a rikicinsu da gwamnatin Buhari
A wani labarin, lauya Pelumi Olajengbesi, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Sunday Adeyemo, shugaban 'yan awaren Yarbawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi murabus daga tawagar kare dan awaren.
Idan baku manta ba, a baya mun kawo muku rahotannin yadda gwamnatin jamhuriyar Benin ta kame Sunday Igboho ta tasa keyarsa magarkama a kasar.
Daga nan ne batutuwa suka fara girma, gwamnatin Najeriya ta fara bibiyar yadda za ta dawo dashi Najeriya don gurfanar dashi.
Asali: Legit.ng