Zamu cigaba da yakar rashin adalci, Buhari ga Firai Ministan Falasdin

Zamu cigaba da yakar rashin adalci, Buhari ga Firai Ministan Falasdin

  • A Habasha, Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da jagoran kasar Falasdin
  • Buhari ya bayyana cewa zai tabbatar da cewa an yi adalci kan abubuwan da ke faruwa a wasu kasashe
  • Firai Ministan Falasdin ya ce akwai bukatar duniya ta san abinda ke aukuwa tsakaninsu da Isra'ila

Addis Ababa - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya bayyana cewa Najeriya zata cigaba da yakar rashin adalci dake gudana a wasu sassan duniya.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin ganawa da Firai Ministan kasar Falasdin, Mohammad Shtayyeh, a taron gangamin shugabannin kasashen Afrika dak gudana a Addis Ababa, Ethiopia.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

A cewar Buhari, zai cigaba da tabbatar da rashin take hakkin bil adama da wasu ke yi.

Kara karanta wannan

Zan cigaba da kula da talakawa har lokacin da na sauka, Buhari

Yace:

"A matsayinmu na kasa, muna iyakan kokarinmu kuma zamu cigaba da ganin an adalci da daidaito ya wanzu."

Shugaban kasan ya bayyanawa Jagoran Falasdinawan cewa Najeriya ba zata daina kira ga zaman lafiya da adalci ba.

Buhari da Firai Ministan Falasdin
Zamu cigaba da yakar rashin adalci, Buhari ga Firai Ministan Falasdin Hoto: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

A nasa jawabin, Firai Ministan Falasdin ya bayyana cewa abinda ke aukuwa tsakanin kasarsa da Isra'ila na sake munana, saboda haka akwai bukatar duniya ta san halin da ake ciki.

Ya yiwa Shugaba Buhari fatan alkhairi da godiya.

Shugaba Buhari ya halarci taron AU a Addis Ababa, birnin kasar Ethiopia

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bude taron gamayyar kasashen nahiyar Afrika watau AU dake gudana yanzu haka a birnin Addis Ababa, ranar Asabar, 5 ga Febrairu, 2022.

Taron ya samu halarci shugabannin kasashen Afrika masu ci da kuma tsaffin shugabannin kasashe.

Kara karanta wannan

Ka tabbatar ka tsare Kaduna kafin ka yi ritaya, Shehu Sani ga Buhari

Hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau, ya saki hotunan shugaba Buhari a taron da mai daukan hoton fadar shugaban kasa, Sunday Aghaeze.

Mun kawo muku cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya shilla Addis Ababa, babbar birnin kasar Ethiopia domin halartan taron gangamin gamayyar kasashen Afrika na 35.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng