Gwamnoni, Sanatoci 63, yan majalisa 106 sun gaza halartan nadin sarautan Amaechi saboda bacin yanayi

Gwamnoni, Sanatoci 63, yan majalisa 106 sun gaza halartan nadin sarautan Amaechi saboda bacin yanayi

Abuja - Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, Sanatoci 62 da yan majalisa 56 sun gaza halartan nadin sarautan Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a garin Daura, jihar Katsina.

Daga cikinsu akwai Sanata Tanko Al Makura da Sanata Ali Modu Sheriff.

Hakazalika akwai tsaffin Sanatocin 42, tsaffin yan majalisar wakilai 50, mataimakan gwamnoni 7, yan majalisar dokokin jiha 13, Jakadun, Sarakunana gargajiya, dss.

Manyan jiga-jigan sun dira babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja amma suka gaza shiga jirgi, rahoton TheNation.

Wata majiya daga hukumar jiragen sama NCAA ta bayyana rashin yanayi matsayin dalilin da yasa jirage suka gaza tashi.

Gwamnoni, Sanatoci 63, yan majalisa 106 sun gaza halartan nadin sarautan Amaechi saboda bacin yanayi
Gwamnoni, Sanatoci 63, yan majalisa 106 sun gaza halartan nadin sarautan Amaechi saboda bacin yanayi
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Ba mu bada sarauta haka kawai: Sarkin Daura yayinda yaiwa Amaechi 'Dan Amanar Daura'

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng