Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci taron AU a Addis Ababa, birnin kasar Ethiopia

Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci taron AU a Addis Ababa, birnin kasar Ethiopia

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bude taron gamayyar kasashen nahiyar Afrika watau AU dake gudana yanzu haka a birnin Addis Ababa, ranar Asabar, 5 ga Febrairu, 2022.

Taron ya samu halarci shugabannin kasashen Afrika masu ci da kuma tsaffin shugabannin kasashe.

Hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau, ya saki hotunan shugaba Buhari a taron da mai daukan hoton fadar shugaban kasa, Sunday Aghaeze.

Shugaba Buhari ya tafi Habasha halartan taron gamayyar kasashen Afrika

Mun kawo muku cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya shilla Addis Ababa, babbar birnin kasar Ethiopia domin halartan taron gangamin gamayyar kasashen Afrika na 35.

Kara karanta wannan

Zan cigaba da kula da talakawa har lokacin da na sauka, Buhari

Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya saki da yammacin Laraba.

Bayan taron, shugaba Buhari zai zauna da wasu shugabannin kasashe kan ganin yadda za'a bunkasa huldar kasuwanci, karfafa tsaro, dss.

Adesina yace Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; Ministan Noma, Mohammed Abubakar; da Ministar tallafi da jin kai, Sadiya Farouq.

Sauran sun hada da NSA Maj. Gen. Babagana Monguno da Shugaban hukumar NIA, Amb. Ahmed Rufai Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng