Har yanzu ba'a biya mu albashi ba, Wasu jami'an Sojojin Najeriya sun jaddada
Sojojin Najeriya da dama sun bayyana cewa har yanzu ba'a biyasu albashin watan Junairu ba duk da jawabin da hukumar ta saki cewa ta biya.
Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya bayyana a jawabin da ya saki ranar Asabar cewa an biya kowani Soja kudin albashinsa na Junairu.
A cewarsa:
"Muna son bayyana cewa a watan Junairu, an biya dukkan albashi da alawus."
Amma wasu Sojoji a sassan Najeriya da suka bukaci a sakaye sunayensu sun bayyana cewa su dai har yanzu babu labar, basu samu albashinsu ba.
TheCable ta ruwaito wani babban jami'in Soja da 2Div Ibadan da cewa:
"Me yasa shugabanninmu basu son fadin gaskiya ne? Har yanzu ban samu albashin Junairu ba, kuma wannan shine gaskiya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Abin takaici ne kuma sai da na karbi bashi don ciyar da iyali ne makonnin baya. Kun san yadda Junairu take kasancewa wani lokacin"
Wani jami'in Soja a 1Div Kaduna yace:
"Babu mutum ko guda a barikin nan da ya samu albashin Junairu."
"La'alla sabbin Sojoji 21 NA ne suka samu amma babu wanda aka biya."
TheCable ta kara da cewa ta tuntubi wasu Sojoji a 3Div dake Jos, kuma wani Soja ya bayyana cewa:
"Hukumar Soja bata biyamu ko sisi ba a shekarar nan."
"Sojoji sun gaji. Bayan aiki, babu kudi."
Tunda Wannan sabon shugaban hafsan ya hau muke samun matsala
Wasu Sojoji sun bayyana cewa tun da aka nada sabon shugaban hafsan Sojin kasa, Laftanan Janar Farouq Yahaya suke samun matsalan albashi.
A cewarsa, tun da ya hau ake musu jinkiri wajen biya.
Wani Soja yace:
"Bamu da takamammen ranar biyan albashi, amma wannan sabon shugaban Sojin zai an shiga sabon wata ake biya."
Sojojin sun ce duk lokacin da sukayi korafi za'a ce musu matsalar na'urar IPPIS da gwamnatin tarayya ta kirkiro ne.
Asali: Legit.ng