Tashin hankali: 'Dan KASTLEA ya kashe direban mota da duka a Kaduna

Tashin hankali: 'Dan KASTLEA ya kashe direban mota da duka a Kaduna

  • Wani direban mota ya riga mu gidan gaskiya a Kaduna sakamakon duka da jami'an hukumar kula da ababen hawa na Kaduna suka yi masa
  • Wasu da abin ya faru a gabansu sun ce an buga wa direban sanda a kansa ne hakan yasa ya fadi daga bisani aka garzaya da shi asibiti inda ya rasu
  • Rundunar yan sandan Jihar Kaduna ta bakin Kakakinta ASP Mohammed Jalige kuma ta bada umurnin a kamo wadanda ke da hannu a lamarin

Kaduna - Jami'in kula da ababen hawa na Jihar Kaduna, KASTLEA, ya halaka wani direba da a riga an bayyana sunansa ba yayin rikici da ya shiga tsakaninsu a Ali Akilu Road, Unguwar Sarki, Kaduna a ranar Juma'a.

Daily Trust ta rahoto cewa lamarin, wanda ya faru misalin karfe 4 na yamma, ya janyo mumunan cinkoson ababen hawa a unguwar da kewaye.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja

Tashin hankali: 'Dan KASTLEA ya kashe direban mota da duka a Kaduna
'Dan KASTLEA ya halaka direban mota da duka a Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Ba bu cikaken bayani game da abin da ya yi sanadin ricikin nasu a lokacin wallafa wannan rahoton, amma ganau sun ce an doki wanda abin ya faru da shi ne a kansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar ganau din, an bugi marigayin da sanda a kansa yayin da suke musayar maganganu.

Yan sanda sun tabbatar da afkuwar lamarin

Kakakin yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa Kwamishinan yan sandan Kaduna, Mudassiru Abdullahi ya bada umurnin a kamo wadanda suka aikata abin.

Ya kara da cewa yan sandan za su gudanar da cikaken bincike a kan lamarin.

Ya ce:

"An samu rashin jituwa tsakanin KASTLEA da wasu direbobi. Sun masa duka sannan aka garzaya da shi asibiti a can kuma ya ce ga garin ku. Don haka, wasu direbobin suka tare manyan hanyoyi domin zanga-zanga amma muka hana su."

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bindige tsohon dan takarar ciyaman da abokinsa

Daily Trust ta gano cewa a yayin da mutumin ya fadi kasa, Jami'an KASTLEA sun bar wurin saboda tsaron kada fusatattun matasa su kai musu hari.

Da aka tuntube shi, Shugaban KASTLEA, Mashal Garba Yahaya Rimi, ya ce bai riga ya samu cikaken bayani kan abin da ya faru ba don haka ba zai iya tsokaci a kai ba.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Kara karanta wannan

Babu wani abu mai suna 'tubabben dan bindiga', kawai a kasheshu: El-Rufa'i

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: