Zan cigaba da kula da talakawa har lokacin da na sauka, Buhari

Zan cigaba da kula da talakawa har lokacin da na sauka, Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taronsa na farko a kasar Habasha ranar Alhamis
  • Buhari ya bayyana jeringiyar abubuwan da zai cigaba da yiwa yan Najeriya don samar da cigaba
  • Mafi muhimmanci ciki, Buhari yace zai kaddamar da kula d jin dadin talakawa da marasa galihu

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a a kasar Habasha ya bayyana cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen fitar da talakawa da marasa galihu daga cikin kangin talauci har ya sauka daga mulki.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayinda gabatar da jawabinsa a taron gamayyar kasashen Afrika AU, mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya bayyana.

Buhari ya ce za'a cigaba da kula da talakawa, tare da inganta sashen ilimi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Zamu shiga yajin aiki, gwamnati ba tada alkawari: ASUU

Zan cigaba kula da talakawa har lokacin da na sauka, Buhari
Zan cigaba kula da talakawa har lokacin da na sauka, Buhari Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Yace:

"Manufar Najeriya shine: Gina tattalin arzikin mai karko; taimakawa marasa galihu da yaye talauci; fadada aikin noma don samar da isasshen abinci; samun isasshen wutan lantarki da man fetur."
"Kara manyan ayyuka da harkar sufuri. inganta kasuwanci da masana'antu; inganta Ilimi, samar da kiwon lafiya, samar da tsaro da samun tsarin yaki da rashawa."
"Najeriya ba zai gushe tana kokarin cimma wadannan manufofi ba duk da kalubalen da rahoton ya bayyana, cikin harda annobar Korona."

Buhari ya kara da cewa gwamnatinsa ba zata daina taimakawa talakawa da marasa galihu ba.

Shugaba Buhari ya tafi Habasha halartan taron gamayyar kasashen Afrika

Mun kawo muku cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya shilla Addis Ababa, babbar birnin kasar Ethiopia domin halartan taron gangamin gamayyar kasashen Afrika na 35.

Kara karanta wannan

Ba na son cin haram, ana biya na kudin da ban yi aiki ba, Hadimin gwamna ya yi murabus

Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya saki da yammacin Laraba.

Bayan taron, shugaba Buhari zai zauna da wasu shugabannin kasashe kan ganin yadda za'a bunkasa huldar kasuwanci, karfafa tsaro, dss.

Adesina yace Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; Ministan Noma, Mohammed Abubakar; da Ministar tallafi da jin kai, Sadiya Farouq.

Sauran sun hada da NSA Maj. Gen. Babagana Monguno da Shugaban hukumar NIA, Amb. Ahmed Rufai Abubakar.

.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng