Rashawa da rashin shugabannin kwarai ke haifar da juyin mulki a Afrika: Amurka

Rashawa da rashin shugabannin kwarai ke haifar da juyin mulki a Afrika: Amurka

  • Babban jami'in Sojan Amurka ya bayyana matsayar kasarsa kan juyin mulkin dake faruwa a Afrika
  • Kwamandan ya ce gaskiya juyin mulkin ba zai rasa alaka da rashin jagororin kwarai da rashawa ba
  • A makon da ya gabata, Sojoji sun yi yunkurin kwace mulki karfi da yaji a kasar Guinea Bissau

Kwamandan rundunar Sojin Amurka dake nahiyar Afrika, Janar Stephen Townsend, ya bayyana cewa rashawa da rashin shugabannin kwarai a matsayin sababin juyin mulki a wasu kasashen Afrika.

A cikin shekaru biyu da suka gabata, an yi juyin mulki a kasashen Mali, Chad, Guine, Sudan da Burkina Faso.

Hakazalika an yi yunkurin yi amma ba'a samu nasara ba a kasar Nijar da Guinea Bissau.

Janar Amurka
Rashawa da rashin shugabannin kwarai ke haifar da juyin mulki a Afrika: Amurka Hoto: Army.mil
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Zan cigaba da kula da talakawa har lokacin da na sauka, Buhari

A ranar Alhamis yayin jawabi da manema labarai ta yanar gizo, Janar Townsend ya bayyana cewa Gwamnatin Amurka na Alla-wadai da juyin mulkin dake faruwa a nahiyar Afrika, rahoton Punch.

A cewarsa:

"Sojoji na rusa demokradiyya a nahiyar Afrika. Ban san iya cewa ga ainihin dalilin da yasa ake juyin mulki a Afrika ba.
"Nahiyar ta kwashe shekaru 20 tana juyin mulki kuma bara mun ga wasu da yawa, amma ina kyautata zaton ba zai rasa alaka da rashin shugabancin kwarai da rashawa ba."
"Amurka bata yarda da canjin gwamnati ta hanyar juyin mulki ba."

Shugaba Buhari ya tattauna da shugaban kasar Guinea kan batun juyin mulki a kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana da shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, wanda sojoji suka yi yunkurin yiwa juyin mulki.

Buhari ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 2 ga watan Fabrairu, a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: