Majalisar Dattawa za ta dauki mataki kan kudin karatun jami'a domin talaka ya samu ilmi

Majalisar Dattawa za ta dauki mataki kan kudin karatun jami'a domin talaka ya samu ilmi

  • Majalisar dattawan Najeriya ta zauna da kungiyar Coalition of Northern Groups Students Wing a Abuja
  • Kungiyar CNG-SW ta hadu da Sanata Ahmad Lawan a kan karin kudin karatun da ake yi a jami’o’i
  • Shugaban majalisar ya yi wa daliban alkawari cewa ba za su bari ayi abin da zai wahalar da dalibai ba

Abuja - Majalisar dattawan Najeriya na kokarin magance matsalar da za a iya fuskanta a harkar ilmin boko a dalilin tashin kudin makaranta a jami’o’i.

A ranar Laraba, 2 ga watan Fubrairu 2020, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce za su iya baki wajen ganin an hana kudin karatun jami’a tashi.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook a yammacin Alhamis, Ahmad Lawan ya ce ya zauna da jagororin gamayyar kungiyar dalibai na CNG-SW.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Miyagu sun sace $4bn daga arzikin Najeriya a 2021, su na sayen makamai

Hadimin shugaban majalisar tarayyan kasar, Ola Awoniyi ya fitar da wannan jawabi a makon nan.

Jamiu Aliyu Charanchi shi ne ya jagoranci tawagar the Coalition of Northern Groups Students Wing (CNG-SW) zuwa gaban shugaban majalisar tarayyan.

Lawan ya karbi kukan matasan, musamman ganin yadda ake neman kara kudin karatu a wasu jami’o’in da ke yankin Arewacin Najeriya a wannan yanayi.

Ahmad Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: Tope Brown
Asali: Facebook

Za mu duba batun nan - Lawan

Sanata Lawan ya ce za su yi wani abu a kan lamarin duba da muhimmancin ilmi. Lawan ya yi alkawari ba za su bari a samu matsala wajen karatu ba.

“Ilmi shi ne jigo da wata al’umma ko jama’a za su cigaba. Kuma duk mutanen da ba su maida hankali a kan ilmi ba, ba za su ga cigaba ba.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro a sakateriyar APC yayin da ake rantsar da shugabannin jihohi

“Tasirin rashin ba ilmi muhimmanci ba zai misaltu ba, baya ga asarar al’umma da za ayi, wasu mutane za su kama layukan da ba su da kyau.”
“Ina ganin cewa a wannan marra, bai kamata ayi karin kudin makaranta ba. Kuma ina ganin dole ne gwamnati ta ba harkar ilmi muhimmanci."

- Ahmad Ibrahim Lawan

Dr. Lawan ya ce ba kafa makarantu ba ne kurum aikin gwamnati, dole a taimakawa dalibai su yi karatu mai nagarta ta yadda za su taimaki al’umma a nan gaba.

“A matsayinmu na Sanatoci kuma wakilan da suke wakiltarku, za mu dauki wannan batu da muhimmanci, za mu sa ido domin a samu mafita.”

Ahmad Ibrahim Lawan

Sanwo Olu ya kai yara makaranta

A ranar Alhamsi ne aka ji labari cewa Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya yi kicibis da wasu mata da suke yawo a lokacin da sa’o’insu su ke aji a makaranta.

Kara karanta wannan

Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

Amarachi Chinedu da Suwebat Husseini za su je kai wa iyayensu markade ne sai gwamnan ya hange su, yanzu maganar da ake yi za a dauki dawainiyar karatunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng